logo

HAUSA

Al’ummun Sudan na rububin sayen dogwayen riguna domin bikin sallah

2022-04-28 10:38:22 CMG HAUSA

 

Yayin da ya rage ’yan kwanaki kalilan a gudanar da bukukuwan karamar sallah, bayan kammala azumin watan Ramadan, al’ummun kasar Sudan sun fara rububin sayen dogwayen rigunan ado da aka fi sani da jallabiya, domin bikin sallah karama.

Al’ummun Sudan da na sauran kasashen dake kewayen kogin Nilu, na amfani da jallabiya a matsayin tufafin kwalliya a lokutan bukukuwa.

A kasar Sudan, ana sanya jallabiya tare da rawani, ko kananan huluna, da wando mai fadi, da kuma takalman Markoub da ake yi da tafun dabbobi.

Jallabiya doguwar riga ce da kan sauka sosai, kuma yawanci na da lau’in fari, da dogon hannu da kewayayyen wuya.  (Saminu)