logo

HAUSA

Hanyoyin mota sun taimaka sosai wajen farfado da yankunan karkara a kasar Sin

2022-04-28 09:33:07 CMG HAUSA

Ya zuwa yanzu tsawon hanyoyin mota da ke cikin yankunan karkara a kasar Sin ya kai kilomita miliyan 4 da dubu 466 baki daya, wadanda suka kawo wa mazauna wurin fiye da miliyan 500. Hanyoyin motar sun aza harsashi mai muhimmanci wajen farfado da yankunan karkara da raya tattalin arzikin yankunan karkara. (Tasallah Yuan)