logo

HAUSA

COVID-19 ta yiwa Amurka mummunar mamaya

2022-04-28 17:27:42 CMG Hausa

Wasu sabbin alkaluma da cibiyar yaki da cututtuka ta Amurka ko CDC ta fitar, sun nuna yadda cutar COVID-19 ta harbi sama da daukacin rabin Amurkawa. Alkaluman sun nuna yadda kaso 58 bisa dari na daukacin al’ummar Amurka, da kaso sama da 75 bisa dari na yara masu karancin shekaru a kasar suka harbu da cutar tun bullar ta kawo yanzu.

Wannan alkaluma sun nuna irin saurin yaduwar nau’in Omicron na cutar tsakanin mutane, wanda hakan ne ya ingiza bazuwar cutar tsakanin Amurkawa. Bincike ya nuna cewa, cikin duk yara hudu, uku daga cikin sun taba nuna alamun kamuwa da wannan cuta.

Annobar COVID-19 ta ci gaba da karuwa a kasar cikin makon jiya, inda adadin masu harbuwa da ita a makon ya karu da kaso 23 bisa dari, da adadin mutane 44,416 a kwana guda. Sai dai adadin masu rasuwa sakamakon cutar ya ragu da kaso 13 bisa dari, idan an kwatanta da makon da ya gabashe shi, inda a makon na jiya adadin ya tsaya kan kimanin mutum 314 a duk rana.

Ita ma jami’ar Johns Hopkins ta bayyana cewa, adadin wadanda suka harbu da cutar COVID-19 a Amurka ya zuwa yanzu, ya haura mutum miliyan 81, kuma tuni cutar ta hallaka mutane 991,940.

Ko shakka babu, bazuwar cutar COVID-19 a Amurka, da irin yadda ta haifar da mummunan tasiri ga rayuwan ’yan kasar ta hanyoyi da dama, wata manuniya ce ga bukatar kara azamar aiwatar da matakan kandagarki, a wuraren da cutar ba ta yaduwa ba, ko yaduwar ta ya dan ragu.

Wani karin darasi da duniya za ta koya game da hakan shi ne rungumar matakan kimiyya cikin gaggawa, a duk lokacin da aka fuskanci barkewar annoba, da fadakar da jama’a hakikanin matakan da suka wajaba a aiwatar ba tare da rufa rufa ba. Kana a yi hadin gwiwa da dukkanin sassa, ta yadda za a gudu tare a tsira tare. (Saminu Hassan)