logo

HAUSA

Waye ke lalata zaman lafiya a kudancin yankin tekun Pasifik?

2022-04-28 21:39:21 CMG Hausa

Kwanan nan ne jaridar The Guardian ta kasar Birtaniya ta wallafa wani bayani, inda ta soki lamirin kasashen Amurka da Australiya saboda wuce gona da irin da suka yi na mayar da martanin da bai dace ba kan yarjejeniyar habaka hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da tsibiran Solomon a fannin tsaro.

Amurka da Australiya sun dade suna yunkurin kawo tsaiko gami da lalata hadin-gwiwar Sin da tsibiran Solomon.

A matsayinta na kasa mai ‘yanci dake yankin tekun Pasifik, tsibiran Solomon yana hada kai da kasar Sin, da zummar tabbatar da zaman lafiya da samar da ci gaba, abun da ya dace da muradun kanta. To, amma me ya sa wannan batu ya janyo babban martani daga Amurka da Australiya?

Dalilin kuwa shi ne, saboda Amurka da Australiya ba su taba mayar da tsibiran kasashe dake yankin tekun Pasifik a matsayin kasashe masu ‘yanci ba, ciki har da tsibiran Solomon, inda suke maida kasashen tamkar ‘yan amshin shatansu. A nasu ra’ayin, su ne za su yanke shawarar da wadanne kasashe, tsibiran tekun Pasifik za su bada hadin-kai, al’amarin da ya shaida ra’ayinsu na nuna babakere da mulkin danniya.

Amma ya dace kasashen Amurka da Australiya su yi tunani cewa, duk wani cikas da suka kawo, me ya sa ba su iya hana tsibiran Solomon da sauran wasu kasashen dake yankin tekun Pasifik su yi hadin-gwiwa tare da kasar Sin ba? Saboda hadin-gwiwar kasar Sin da wadannan kasashe, hadin-gwiwa ce da aka yi bisa adalci, ba tare da gindaya wani sharadin siyasa ba, kana yana taimakawa sosai wajen kyautata rayuwar mazauna wurin.

Abun da ya kamata kasashen Amurka da Australiya suka yi shi ne, girmama ‘yancin kai na tsibiran kasashe dake yankin tekun Pasifik, kana, ya kamata kasashen dake kawo barazana ga sauran kasashe da lalata zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar, su fice daga wannan yanki na kudancin tekun Pasifik ba tare da bata lokaci ba. (Murtala Zhang)