logo

HAUSA

Mu rungumi karanta litattafai maimakon wayar salula

2022-04-27 09:27:00 CMG Hausa

A ranar 23 ga watan Afrilu ne, aka yi bikin Ranar karanta litattafai ta kasar Sin da ranar kare ’yancin mallakar fasaha ta kasa da kasa. Rana ce da hukumar raya ilimi, kimiya da al’adu ta MDD (Unesco) ta kebe a kowace shekara, don bunkasa batutuwan da suka shafi karance-karance da wallafe-wallafe, da ’yancin mallakar fasaha.

Ana kuma murnar bikin wannan rana, don karrama mawallafa da ma litattafan da aka wallafa, da yayata muhimmamcin karanta litattafai da kare ’yancin mallakar fasaha.

Albarkacin wannan rana, cibiyar nazarin dab’in labarai ta kasar Sin ta fitar da sakamakon binciken da aka yi game da karanta litattafai na al’ummun Sinawa karo na 19 a yayin babban taron karanta litattafai karo na farko da aka shirya a wannan rana, inda aka bayyana cewa, adadin litattafan da kowane Basine da ya kai shekarun haihuwa 18 ya karanta a shekarar 2021 ya kai guda 4.76, adadin litattafan da ya karanta ta yanar gizo ya kai guda 3.3, duka sun karu bisa na shekarar 2020.


Kana adadin litattafan da kowane Basine wadanda ba su kai shekarun haihuwa 17 ba ya karanta, ya kai guda 10.93, adadin da ya karu da 0.22, idan aka kwatanta da shekarar 2020.

Shugaban kasar Xi Jinping ya aike wa babban taron wasikar taya murna, inda ya bayyana cewa, yana fatan daukacin al’ummun Sinawa za su kara mayar da hankali wajen karanta litattafai.


Masharhanta dai na danganta rashin karanta litattafan kan tasirin fasahohin zamani, kamar Intanet da wayoyin salula da sauransu. Matakin da ko kadan ba zai haifar da da mai ido ga ci gaban wanzuwar dakunan karatu ba, da dabi’ar karance-karance da wallafe-wallafe, lamarin da ka iya darkushe kuzarin marubuta a nan gaba. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)