logo

HAUSA

Ana Kukan Targade..

2022-04-27 17:21:15 CMG Hausa

A yayin da duniya ke ci gaba da fama da annobar COVID-19, a hannu guda kuma hukumomi da masana a fannin yaki da sauyin yanayi, na yin gargadi game da yadda yunwa da fari za su iya addabar sassan duniya. “Wai ana kukan targade sai ga karaya”. 

Sanin kowa ne cewa, masana sun sha yin kashedi tun kafin bullar annobar cutar COVID-19 ta zama wani batu na daban cewa, za a fuskanci mummunan matsalar jin kai da ba a taba gani irinta ba, tun a lokacin yakin duniya na biyu, saboda wasu dalilai.

Na baya-bayan shi ne, kiran da sama da hukumomin agaji 50 suka yi na gaggauta samar da karin kudade da shugabanci na gari don tinkarar gagarumar matsalar ayyukan jin kai dake fuskantar miliyoyin mutanen dake zaune a shiyyar gabashin Afrika sanadiyyar matsanancin fari, har ma aka yi kashedin cewa, muddin aka yi jinkiri, babu makawa rayukan jama’a da dama na iya salwanta.

Kungiyar agaji ta Save the Children, da Norwegian Refugee Council, da gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu a Somaliya, na daga cikin wadanda suka bayar da wannan gargadi, gabanin taron kungiyoyin bada tallafi na kasa da kasa da za a gudanar a Geneva. Tuni ma alkaluma suka nuna cewa, sama da mutane miliyan 14 a kasashen Somaliya, da Habasha da Kenya, kuma kusan rabin adadin kananan yara ne, sun riga sun tsunduma cikin mummunan yunwa.

Matsalolin tashe-tashen hankula, da rashin tsaro, da karayar tattalin arziki, suna daga cikin dalilan dake kara ta’azzara wannan matsala na tsawon shekaru. Yanzu kuma ga batun matsalar sauyin yanayi, da yadda tarin jama’a ke kauracewa muhallansu, lamarin dake sanadiyyar fadawar karin mutane cikin yanayin tsananin bukata.

Ganin irin mummunan halin da aka shiga, ya sa masu fashin baki ke cewa, yanzu ne lokacin da ya dace na daukar matakai, domin kaucewa fadawar miliyoyin al’ummomin dake shiyyar gabashin Afrika cikin fitina. Tun kafin wankin hula ya kai dare. (Ibrahim Yaya)