Kyautar da kasar Sin ta baiwa duniya ba kwayar maganin artemisinin ba ne kawai
2022-04-26 21:33:21 CMG Hausa
Shekarar 2022 shekara ce ta cika shekaru 50 da gano kwayar maganin artemisinin. Shekaru 50 da suka wuce, masana kimiyya na kasar Sin da Tu Youyou ta wakilta, sun gano tare da samun nasarar hako sinadarin artemisinin, wanda ya taimaka wa kasar Sin wajen kawar da malariya baki daya. Kasar Sin ta kuma yada wannan magani mai kyau zuwa duniya baki daya. Kimanin mutane miliyan 240 ne a yankin kudu da hamadar Sahara suka amfana da maganin artemisinin, wanda ‘yan Afirka ke kira da “Sihirin magani daga gabas mai nisa”.
Ban da artemisinin, al'ummar Afirka da dama na tunawa da cewa, a lokacin da nahiyar Afirka ta yi fama da annobar Ebola, wasu kasashe da yawa sun janye daga yankin da annobar cutar ta bulla, amma a nata bangare nan da nan kasar Sin ta aike da tawagar likitoci don taimaka wa Afirka, ta kuma aike da muhimman kayayyakin da ake bukata ga nahiyar, kana sun hada kai kafada da kafada tare da kasashen Afirka don yaki da cutar har karshe.
A yanzu haka, bil'adama na fuskantar annoba mafi muni da ba a taba gani ba shekaru dari da suka wuce. Kamar yadda ta ba da gudummawar artemisinin ga duniya, Sin ta kara taimakawa duniya tare da kaddamar da aikin jin kai na gaggawa mafi girma. Mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Masar Muhammad Hassan ya bayyana cewa, “Kasar Sin tana sa himma wajen ba da taimakon rigakafi ga sauran kasashe. Sakamakon hadin gwiwar likitocin tsakanin kasashen biyu, adadin al’ummar da aka yi musu allurar rigakafi a kasar Masar ya kai kashi 70 cikin 100.”
Daga artemisinin har zuwa alluran rigakafin COVID-19, dukkansu sun rubuta labari iri daya game da yadda kasar Sin da duniya ke hadin kai don kawar da matsaloli. Kasar Sin ta sani sarai cewa, ba wai kasashe daban daban suna cikin kananan jiragen ruwa sama da 190 ba ne, a'a suna cikin wani babban jirgin ruwa mai makoma daya. A yayin da ake fuskantar matsalar rashin lafiyar jama'a a duniya, ta hanyar gina al'ummar lafiyar bil'adama ta bai daya ne kawai za mu iya shawo kan cutar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)