logo

HAUSA

Labarin Likitocin Beijing Da Suka Samar Da Agajin Jinya Ga Mutanen Afirka

2022-04-26 15:29:15 CMG Hausa

Tun shekaru sama da 50 da suka gabata, ya zuwa yanzu, kasar Sin take aiwatar da ra’ayin gina al’umma mai kaykkyawar makoma ta bai daya a fannin kiwon lafiya, don tabbatar da koshin lafiyar jama’a. A shekara ta 1963, kasar Sin ta tura tawagar ma’aikatan jinya ta farko zuwa nahiyar Afirka. Kawo yanzu, akwai ma’aikatan jinyar kasar Sin da dama wadanda aka tura zuwa Afirka don kulawa gami da samar da magani ga mutanen Afirka, inda aka jinjina musu saboda jajircewarsu wajen kare rayukan al’ummar wurin. Har ma ana kiran likitocin kasar Sin da suna “mala’ikar kasar Sin sanye da kayan likitoci”.

Waiwaye adon tafiya. Tun a shekara ta 1968 ne, hukumar birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, ta fara tura wata tawagar ma’aikatan jinya 36 zuwa kasashen waje. Kawo yanzu, cikin shekaru 54, gaba daya hukumar birnin Beijing ta tura irin wadannan tawagogi 53 zuwa kasashe da yankuna 11 a duk fadin duniya. Daga cikin ma’aikatan jinyar 1011, har akwai guda 12 wadanda suka sadaukar da rayukansu a kasashen da suka yi aikin samar da tallafi. A kasashen waje, ba kulawa da marasa lafiya kawai ma’aikatan jinyar kasar Sin suka yi ba, har ma sun yi kokarin kafa asibitoci da dakunan gwaje-gwaje, tare kuma da horas da ma’aikatan jinyar wurin, al’amarin da ya sa suka kulla zumunci mai zurfi tare da jama’ar wurin.

A watan Agustar shekara ta 2021, an kafa tawagar ma’aikatan jinyar kasar Sin karo na 29 da suka je kasar Guinea don samar da tallafi, inda kuma aka ba su horo a fannoni daban-daban, ciki har da yaren Faransanci, da ka’idojin harkokin waje da sauransu. Daga cikin ma’aikatan jinyar guda 22, akwai 20 wadanda suka zo daga asibitin Tiantan dake birnin Beijing. A nasa bangare, shugaban asibitin, Wang Yongjun ya bayyana cewa, a lokacin da cutar mashako ta COVID-19 ke ci gaba da addabar duniya, tawagar ma’aikatan jinyar kasar Sin ta tafi Guinea don samar da tallafi, abun da ya sa suka cancanci yabo matuka.

A ranar 6 ga watan Maris din bana, wadannan ma’aikatan jinyar kasar Sin sun isa Conakry, fadar mulki kasar Guinea, inda suka fara aikin samar da agajin jinya har na tsawon watanni 18. Shugaban tawagar ma’aikatan jinyar kasar Sin karo na 29 da suka je Guinea, Mista Guo Wei ya ce, ban da samar da agajin jinya, likitocin kasar Sin za su fadada hadin-gwiwa tare da takwarorinsu na kasar, a fannonin da suka shafi kiwon lafiya, kula da harkokin asibiti, gyare-gyare ga likitanci da sauransu.

Zhang Wei shi ne shugaban tawagar ma’aikatan jinyar kasar Sin karo na 28 da aka tura zuwa Guinea, ya waiwayi ayyukan da tawagarsa ta yi a Guinea, inda ya ce, yaduwar cutar COVID-19, gami da wasu cututtuka, ciki har da maleriya. da shawara, da Ebola, da kyanda, duk sun haifar da kalubale ga rayuwar jama’ar kasar.

Tawagar ma’aikatan jinyar kasar Sin karkashin shugabancin Zhang Wei, ta yi namijin kokari don hada kai tare da cibiyoyin kiwon lafiya na Guinea, a fannin musanyar fasahohin aikin jinya, da samar da kayayyaki da horo kyauta, abun da ya taimaka sosai ga dakile yaduwar cututtukan COVID-19 da Ebola a kasar.

Mista Zhang Wei ya kara da cewa, zuwa watan Maris din shekara ta 2022, an kafa kwamitin dakile cututtuka masu yaduwa a asibitin sada zumunta na Sin da Guinea, da samar da horo ga ma’aikatan asibitin a fannin hana yaduwar cututtuka, da ilimin da ya shafi sanya takunkumin baki da hanci da tsabtace wurin aiki da sauransu.

Idan mun dubi tarihin samar da agajin jinya da likitocin birnin Beijing na kasar Sin suka yi a kasashen ketare, tun a ranar 8 ga watan Yunin shekara ta 1968, Wang Huaiqing da sauran wasu kwararrun aikin jinya daga cibiyoyi daban-daban na Beijing, sun yi tattaki zuwa kasar Guinea dake yammacin Afirka, inda suka bude babin samar da agajin jinya da ma’aikatan Beijing suka yi.

Daga bisani, akwai likitocin Beijing masu tarin yawa, wadanda suka bayar da hidimomin jinya ga kasashe daban-daban, ta hanyoyin bada magani, da kula da marasa lafiya, da dakile yaduwar cututtuka, da samar da kyautar kayan aikin likita da fadakar da al’umma kan likitancin gargajiyar kasar Sin da sauransu. Har wa yau, likitocin Beijing sun horas da dimbin ma’aikatan jinyar kasashen waje, musamman na Afirka, don inganta kwarewarsu a fannin aikin jinya.

A shekara ta 2014, cutar Ebola ta barke a kasashen Afirka daban-daban. A nasa bangaren, shugaban tawagar ma’aikatan jinyar da kasar Sin ta tura zuwa Guinea karo na 23, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban asibitin Anzhen na Beijing, Kong Qingyu ya bayyana cewa, a wancan lokaci, likitoci ba su fahimci cutar sosai ba, sun dai san cuta ce kawai mai saurin yaduwa, amma babu wani takamammen magani.

Lokacin da cutar Ebola ta barke a yammacin Afirka, ya zo daidai da lokacin da tawagar likitocin kasar Sin karo na 23 ke shirin kammala ayyukansu baki daya a Guinea. Amma likitocin kasar Sin sun zabi su ci gaba da aiki a kasar.

Kong Qingyu ya ce, ba tare da bata lokaci ba, tawagar ta tuntubi hukumomin lafiya na kasar Sin don neman samun taimako, da nazarin sabbin bayanan da aka turo daga kasar Sin, don fadakar da al’ummar Guinea kan ilimin kandagarkin cutar Ebola. Haka kuma a lokacin, an riga an kafa tawagar ma’aikatan jinyar kasar Sin karo na 24, masu shirin zuwa Guinea don samar da agajin jinya. Shugaban tawagar, mai kwararrun likitoci 19 daga asitibin zumunta na Beijing, Wang Zhenchang ya ce, bayan da cutar Ebola ta barke, akwai kasashe da dama da suka janye jari da mutanensu daga Afirka, tawagarsa karo na 24 ita ma tana da zabi biyu. Wang ya ce, idan ba su je ba, tawagar da ta riga ta kammala aiki ba za ta iya dawowa kasar Sin ba, shi ya sa ya zama dole sabuwar tawagar ma’aikatan jinyar kasar Sin kashi na 24 ta tafi can kasar Guinea don dakile annobar tare da al’ummar kasar.

A ranar 16 ga watan Agustar shekara ta 2014, kashin farko na tawagar ma’aikatan jinyar kasar Sin karo na 24 karkashin jagorancin Wang Zhenchang sun isa kasar Guinea, inda suka kaddamar da aikin dakile yaduwar cutar Ebola ba tare da wani jinkiri ba. Baya ga aikin kula da masu kamuwa da cutar gami da ba su magani, ma’aikatan jinyar kasar Sin sun samar da horon kiwon lafiya ga takwarorinsu sama da 1700 na kasar Guinea, ciki har da akawun gwamnatin kasar, wadanda suka canja ra’ayinsu tare da daukar matakan da suka dace wajen yaki da annobar Ebola a kasar.

Dangane da hadin-gwiwar kasashen Sin da Guinea kuwa, wani muhimmin abun da ba za manta da shi ba shi ne, asibitin sada zumunta tsakaninsu, wanda aka fara amfani da shi tun a watan Afrilun shekara ta 2012. Sakamakon goyon bayan tawagogin ma’aikatan jinyar kasar Sin, an kara kafa sassa daban-daban a asibitin, abun da ya sa asibitin ya zama kan gaba a duk fadin kasar Guinea.

Wang Yu shi ne shugaban tawagar ma’aikatan jinyar kasar Sin da aka tura zuwa kasar Guinea karo na 25, kana mataimakin asibitin Tongren na Beijing. Wang ya bayyana cewa, lokacin da suka isa Guinea a watan Janairun shekara ta 2016, an kusan kawo karshen yaduwar cutar Ebola, kuma daya daga cikin muhimman ayyukansu a lokacin shi ne, taimakawa wajen ganin an gina sashin kula da masu fama da cututtuka masu tsanani, inda ma’aikatan jinyar kasar Sin suka fara horar da takwarorinsu na asibitin sada zumunta na Sin da Guinea, da nuna musu yadda za’a kula da masu fama da cututtuka masu tsanani a zahirance.

watan Satumbar shekara ta 2020, yayin da cutar mashako ta COVID-19 ke yaduwa a duk fadin duniya, kasar Sin ta tura tawagar ma’aikatan jinyarta karo na 28 zuwa kasar Guinea, wadda ke kunshe da kwararrun likitoci daga hukumar kiwon lafiya ta Beijing, da asibitin Xuanwu na Beijing, gami da cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Beijing. Shugaban tawagar ma’aikatan jinyar kasar Sin karo na 28 da aka tura zuwa Guinea, Zhang Wei ya ce, kula da marasa lafiya a wurin ba abu ne mai wahala sosai ba, abu mai wuya shi ne yadda likitocin kasar Sin za su koyawa takwarorinsu na wurin fasahohin aikin jinya. Domin cimma wannan buri, likitocin kasar Sin sun bi hanyoyi daban-daban don inganta kwarewar likitocin Guinea. A ranar 19 ga watan Janairun shekarar da muke ciki, an kafa cibiyar kula da jijiyoyin dan Adam, da cibiyar kula da marasa lafiya daga nesa, gami da dakin gwaji na jijiyoyin dan Adam a asibitin sada zumunta na Sin da Guinea, al’amarin dake da babbar ma’ana ga ci gaban harkokin kiwon lafiya a kasar.

Yanzu asibitin sada zumunta na kasashen Sin da Guinea ya zama abin koyi ga muhimmin aikin fadada hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin gina asibitoci, kuma dalilin jajircewar likitocin birnin Beijing, an kara raya asibitin sada zumunta na Sin da Guinea don zama cibiyar aikin jinya a yammacin Afirka, ta yadda karin al’ummar nahiyar Afirka za su amfana.

Wani babban jami’in dake aiki a hukumar kiwon lafiya ta birnin Beijing mai suna Zhong Dongbo ya ce, tun lokacin da Beijing ta fara tura tawagar ma’aikatan jinya zuwa ketare a shekara ta 1968, ya zuwa yanzu, an canja ma’aikatan jinya daga tsoffi zuwa sabbi, amma abun da ba’a canza ba shi ne dadadden zumunci tsakanin al’ummomin Sin da Afirka, da kuma ra’ayi iri daya, wato gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Murtala Zhang)