logo

HAUSA

Malariya na kashe mutane 200,000 duk shekara a Najeriya

2022-04-26 11:06:06 CMG HAUSA

 

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar cewa, mutane 602,020 ne suka mutu a sanadiyyar cutar malaria a Afrika a bara.

Taken ranar yaki da cutar Malariya ta duniya na shekarar 2022 shi ne, “Amfani da sabbin dabarun rage hadarin cutar malariya da ceton rayuka". Kwararru sun nuna damuwa, sai dai kuma, duk da kokarin da ake yi na dakile cutar malariyar, Najeriya tana hasarar sama da dala biliyan 1.1 a duk shekara a aikin kandagarki da kula da masu fama da cutar, sannan duk da daukar wadannan matakai, a kalla mutane 200,000 ne cutar ta hallaka a Najeriya, sannan wasu mutane miliyan 61 sun kamu da cutar malariyar a shekarar 2021. Bugu da kari, kasashen Najeriya, da Kongo DRC, da Tanzania da Mozambique, su ne ke da sama da rabin adadin mutanen da cutar malariyar ta kashe.

Hukumar WHO ta yi kira ga kasashen duniya, da su zuba jari, da kirkiro sabbin fasahohi wajen bullo da sabbin hanyoyin dakile yaduwar cutar, da binciken masu fama da cutar, da amfani da magungunan cutar, da sauran dabarun samun nasarar yaki da cutar malariyar. (Ahmad Fagam)