logo

HAUSA

An shirya taron murnar “Ranar Harshen Sinanci Ta Kasa Da Kasa” ta intanet A Liberiya

2022-04-26 10:22:16 CMG HAUSA

 

A ranar 25 ga watan Afrilu, ofishin jakadancin kasar Sin a Liberiya, da cibiyar koyar da al’adun kasar Sin ta Confucius a jami’ar Liberiya, sun shirya taron hadin gwiwa na murnar “Ranar Harshen Sinanci Ta Kasa Da Kasa” ta shekarar 2022 ta intanet game da koyar da yaren Sinanci a yammacin Afrika.

Jakadan kasar Sin a Liberiya, Ren Yisheng ya bayyana a jawabinsa cewa, ya kamata dukkan kasashe su yi watsi da dukkan al’adu ko kuma tunanin kawo baraka, kana a yi kokarin daukar kwararan matakan tabbatar da zaman lafiyar duniya, da cudanya, da koyi da juna game da al’amurran dake shafar wayewar kan bil adama. Ana fatan cewa, kasashen Afrika, da daliban kasar Liberiya za su yi kokarin karfafa mu’amala da abokantaka a tsakanin Sin da Afrika, da kuma tsakanin Sin da Liberiya ta hanyar neman kwarewa a yaren Sinanci da al’adun Sinawa. Kasar Sin a shirye take ta yi aiki da dukkan bangarori da suka hada da Liberiya, domin daga matsayin hulda a tsakanin mutum da mutum, da zurfafa hakikanin hadin gwiwa, da ba da gudunmawa wajen gina kyakkyawar makomar bil adama ga al’ummun Sin da Afrika.

Yanayin taron karawa juna sanin ya kasance mai kayatarwa da kyakkyawar abota. Malamai da dalibai na kwalejin Confucius dake jami’ar Liberiya, sun gabatar da shirye-shirye masu ban mamaki, kamar wakoki da raye-raye, da wasannin gargajiya na Chinese Kunfu, da jawabai, da rera wakoki tare a tsakanin dukkan mahalarta taron ta intanet. (Ahmad)