logo

HAUSA

Uganda da Rwanda sun kulla yarjejeniyar yakar matsalar tsaro a gabashin Kongo DR

2022-04-25 11:29:29 CMG Hausa

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, da na kasar Rwanda, Paul Kagame, a ranar Lahadi sun cimma matsayar kulla yarjejeniyar hadin gwiwa don tabbatar da tsaro da zaman lafiyar shiyyar, domin shawo kan yanayin da ake ciki a jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC.

Museveni ya ce, matsalolin dake addabar shiyyar kamar rikicin Kongo Kinshasa, yana bukatar daukar matakai daga bangarori da dama, na dukkan mambobin kasashen shiyyar gabashin Afrika, wanda ya kunshi kasashen Uganda da Rwanda da Tanzania da Kenya da Burundi da Sudan ta kudu, da jamhuriyar Kongo DRC, kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar a ranar Lahadi.

Museveni ya ce, a wannan karo, tilas ne a yi aiki tare, duba da yadda mutane ke matukar dandana kudarsu. Ya ce, ya fadawa shugaba Kenyatta cewa, muddin aka gaza dunkulewa a matsayin shiyya guda, to mai yiwuwa ne Kongo Kinshasa za ta iya komawa tamkar Sudan. Ya ce shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya jagoranci taron tattaunawar shugabannin kasashen shiyyar a Nairobi, a ranar Alhamis game da batun yanayin da ake ciki a Kongo DRC.

Shugaba Kagame yace, dole ne shugabanni da dukkan masu ruwa da tsaki su tattauna game da yadda za a kawo karshen rikicin Kongo. (Ahmad)