logo

HAUSA

Hukumar sojin kasar Iran ta shirya bukukuwan farentin soja domin murnar ranar kafa rundunar sojin kasar

2022-04-25 09:00:57 CMG Hausa

Ran 18 ga watan Afrilu, rana ce ta murnar kafa rundunar sojin Iran. Sabo da haka, a sassan daban daban, hukumar sojin kasar Iran ta shirya bukukuwan farentin soja domin murnar ranar. A Tehran, babban birnin kasar Iran, an yi amfani da dimbin tankunan yaki, da igogin wuta da na’urorin lantarki da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka da na’urorin Rada da jiragen sama masu saukar ungulu a yayin bikin. Shugaban kasar Iran Seyed Ebrahim Raisi da wasu muhimman hafsoshin sojin kasar sun halarci bikin a Tehran. (Sanusi Chen)