logo

HAUSA

Kowa ya samu ci gaba ya tuna da dan uwansa

2022-04-25 21:24:25 CMG Hausa

Yau rana ce ta yaki da zazzabin cizon sauro Malariya. Wannan cuta tana haifar da mummunar barna a duniya. A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO, mutane miliyan 241 sun kamu da cutar a shekarar 2020, yayin da wasu dubu 627 daga cikinsu sun mutu. Kana yawancin mutanen da suka kamu da cutar, da wadanda suka rasa rayuka sakamakon cutar, ‘yan kasashen Afirka ne.

Kasar Sin ita ma ta yi fama da cutar Malariya sosai a baya. A shekarun 1940, kasar Sin ta kan sanar da kamuwar mutane kimanin miliyan 30 da Malariya a duk shekara. Sai dai zuwa yanzu, an riga an kawar da cutar daga kasar Sin: A shekarar 2021, bayan da ba a samu ko da mutum daya da ya kamu da cutar ba a kasar cikin wa’adin wasu shekaru 4 a jere, ya sa ta samu tabbaci daga hukumar WHO cewa, an yi nasarar kawar da cutar baki daya cikin kasar.

Ta yaya kasar Sin ta cimma wannan nasara? Amsar ita ce kokarin daukar dabaru masu dacewa a kai a kai. Wasu shekaru 50 da suka wuce, masu nazarin kimiya da fasaha na kasar Sin sun gano sinadarin Artemisinin, inda suka fara sarrafa magani da shi. Zuwa yanzu magunguna masu kunshe da Artemisinin sun zama dabara mafi kyau da ake yin amfani da ita wajen jinyar mutanen da suka kamu da cutar Malaria. Kana kasar ta dauki wasu matakai irinsu raba gidan sauro, da fasahohi na kashe sauro, don dakile cutar Malaria.

Abokai da suka fahimci manufofin kasar Sin a fannin hulda da kasashen waje sun san cewa, kasar Sin ba ta yin babakere a fannin fasahohi don kare moriyar kai. Bayan da kasar ta samu fasahohin da ake bukata wajen dakile cutar Malaria, ta fara taimakawa kasashe masu tasowa, ta hanyar ba su magunguna, da tura musu kwararrun likitoci, da horar da ma’aikata, da dai sauransu. Daga shekarar 2012 zuwa yanzu, kasar Sin ta aiwatar da manyan ayyuka na tallafawa sauran kasashe fiye da 300, da gina cibiyoyin dakile yaduwar Malaria kyauta a kasashe 30, da tura kwararrun likitoci dubu 28 zuwa kasashe da yankuna 72, inda aka horar da ma’aikata masu fasahar dakile cutar Malaria fiye da dubu 10.

A kasar Sao Tome da Principe, a kan samu mutane dubu 2 zuwa 3 da suka kamu da cutar Malaria a kowace shekara. Sai dai, yanzu haka, wata kungiyar likitoci ta kasar Sin tana gudanar da aikin dakile cutar a cikin wasu kauyukan kasar. A safiyar kowace rana, likitocin Sin da abokan aikinsu ‘yan kasar Sao Tome da Principe su kan shiga kauyukan, don gudanar da gwajin jinin mazauna kauyukan. Idan an ga mutum ya kamu da cutar Malaria, za a ba shi magani don ya sha nan take. Sa’an nan zuwa dare, za su shiga dajin dake kewayen kauyukan, inda za su fesa ruwan magani don kashe sauro. Ta wadannan dabaru, sannu a hankali aka fara shawo kan yanayin yaduwar cutar Malaria a kasar.

Sai dai me ya sa kasar Sin ke son raba fasahohinta na dakile cutar Malaria tare da sauran kasashe? Dalili shi ne, kasar Sin na da manufar kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya, wadda ta sa take lura da bukatu na sauran kasashe, musamman ma a fannin raya kasa. A ganin kasar, idan ita kadai ta samu ci gaba, to bukatarta ba ta biya ba, kana kowa ya samu ci gaba ya tuna da dan uwansa.

A wannan lokaci na watan Ramadan mai tsarki, ya kamata mu yi addu’a da fatan Allah ya sa mu amfana da juna, da fatan za mu kawar da cutar Malaria a ko ina cikin sauri. (Bello Wang)