logo

HAUSA

Jihar Imo dake kudancin Najeriya ta sha alwashin rufe haramtattun matatun mai bayan wata fashewa

2022-04-25 10:52:35 CMG Hausa

Mahukunta a jihar Imo dake kudancin Najeriya sun sha alwashin rufe dukkanin haramtattun matatun mai da wasu ba ta gari ke kafawa a asirce, bayan da wata fashewa, a daya daga irin wadannan matatu ta hallaka mutane sama da 100 a daren ranar Juma’ar.

Da yake bayyana hakan cikin wata sanarwa, kwamishinan watsa labarai na jihar Declan Emelumba ya ce, gwamnati ta yi matukar damuwa da aukuwar fashewar, tuni kuma aka kafa wani kwamiti na musamman, domin tabbatar da nasarar matakan dakile sake aukuwar hakan a nan gaba.

Mr. Emelumba ya ce a madadin kwamishinan albarkatun mai na jihar Goodluck Opiah, suna sane da yadda bata gari ke aikata laifuka masu nasaba da satar albarkatun mai a jihar ta Imo, da ma wasu jihohin yankin “Niger Delta” masu arzikin mai. Don haka gwamnati za ta yi hadin gwiwa da sojojin kasar, wajen rushe irin wadannan matatun mai marasa lasisi.

Yayin ziyarar da ya kai garin Abacheke, kusa da inda aka samu fashewar, kwamishinan albarkatun mai na jihar Goodluck Opiah ya shaidawa manema labarai cewa, laifuka masu nasaba da kafa matutu ba bisa ka’ida ba, suna gurgunta tattalin arzikin jihar, don haka za su ci gaba da aikin wayar da kan al’umma game da munin hakan, tare da aiwatar da tsauraran matakan dakile su. (Saminu)