logo

HAUSA

Kongo Kinshasa ta ayyana bullar sabuwar annobar Ebola

2022-04-24 16:52:03 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da cewa, jamhuriyar demokaradiyyar Congo ta ayyana bullar kwayar cutar Ebola a karo na 14 bayan tabbatar da samun rahoton bullar cutar guda daya a Mbandaka, wani birni dake lardin Equateur a arewa maso yammacin kasar.

Matshidiso Moeti, darektar hukumar WHO mai kula da shiyyar Afrika, tace, cutar ta fara bayyana ne tun makonni biyun da suka gabata, kuma a halin yanzu suna kokarin daukar matakan dakile ta. Moeti ta ce, wani labari mai faranta rai shi ne, hukumomin lafiyar jamhuriyar demokaradiyyar Kongo suna da kwarewa sama da kowa a duniya wajen daukar makatan dakile annobar Ebola cikin gaggawa.

Wannan shi ne karo na 14 da aka samu bullar cutar Ebola a kasar ta jamhuriyar demokaradiyyar Kongo, tun bayan samun rahoton bayyanar annobar karo na farko a shekarar 1976. Sannan kuma wannan shi ne karo na shida da aka samu bullar cutar daga shekarar 2018, kuma shine yanayin da aka fi samun bullar cutar akai-akai a tarihin cutar Ebola a kasar. A lokutan baya ma, lardin Equateur ya fuskanci bullar annobar a shekarun 2020 da 2018, inda aka samu rahoton bullar cutar 130 da kuma 54.(Ahmad)