Japan, ki yi hattara!
2022-04-24 21:36:16 CMG Hausa
Yau shekara guda kenan da ta gabata, gwamnatin kasar Japan ta sanar da kudurinta na zubar da dagwalon ruwan tashar nukiliya ta Fukushima a cikin teku. A kwanan nan kuma, kamfanin samar da wutar lantaki ta Tokyo, wato (Tokyo Electric Power), ya kare aniyarta na fara gina mafitar dagwalon ruwa a karkashin teku, ba tare da yin la’akari da nuna adawa ko kuma rashin amincewar da gamayyar kasa da kasa, da ma al’ummar kasar suka nuna ba. An ce, za a fara zubar da ruwan a farkon shekarar 2023.
Sakamakon igiyar ruwa mafi karfi da ake samu a mashigar tekun Fukushima, an ce da zaran an zubar da ruwan, zai iya yaduwa zuwa sama da rabin tekun Pasifik cikin kwanaki 57, da ma tekunan duniya baki daya cikin shekaru 10. Ba za a iya kawar da kai daga mummunan tasirin da zai iya haifarwa ga yanayin teku da ma tsaron abinci da kuma lafiyar bil Adama ba. Zubar da dagwalon ruwa ba batu ne da ya shafi kasar Japan ita kadai ba, sai dai batu ne da ya shafi duniya baki daya.
Japan, ki guji daukar mataki na son kai! (Mai Zane: Mustapha Bulama)