logo

HAUSA

Sama da mutane 100 sun mutu a fashewar wata haramtacciyar matatar mai a Najeriya

2022-04-24 17:28:32 CMG Hausa

Wata majiya ta bayyana cewa, sama da mutane 100 ne suka mutu a sakamakon fashewar wata matatar mai da aka gina ba bisa ka’ida ba, a jahar Imo dake kudancin Najeriya.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma’a a wata haramtacciyar matatar man fetur a karamar hukumar Egbema dake jahar, a kan iyakokin jahohin Imo da Rivers, an tabbatar da hasarar rayuka 100 kawo yanzu.

A cewar shugaban yankin, kana shugaban majalisar koli mai kula da albarkatun mai da iskar gas na jahar Imo, Collins Ajie, an samu fashewar ne ba zato ba tsammani a cikin wani daji dake tsakanin jahohin Imo da Rivers, sannan wani mummunan hayaki ya tirnike dukkan yankin.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho, Ajie ya ce, abin takaici ne, kuma babu wanda ya tsammaci faruwar hadarin wanda yayi sanadiyyar konewar mutane 108 ya zuwa yanzu.

Irin wadannan haramtattun matatun mai suna gudanar da ayyukansu ne  ta hanyar satar danyen mai daga bututan mai mallakin kamfanonin hakar mai, sannan suna tace man ne a wasu kananan tankokin mai.

Fasa bututan mai da satar mai ya zama ruwan dare a Najeriya, lamarin dake haifar da mummunar hasara ga tattalin arzikin kasar.(Ahmad)