logo

HAUSA

​Nollywood ta shirya fina-finai 541 a rubu’in farko na bana

2022-04-23 17:06:18 CMG Hausa

Kamfanonin shirya fina-finai na Najeriya Nollywood, sun shirya fina-finai 541 a rubu’in farko na shekarar 2022, inda ya karu da kashi 41.6 bisa 100 daga adadin fina-finai 382 da aka shirya a rubu’in da ya gabata. Hukumar tace fina-finai da bidiyo ta kasar (NFVCB), ta sanar da hakan a ranar Juma’a.

NFVCB, hukuma ce ta gwamnati, wadda aka dorawa alhakin tsara dokokin tacewa da lura da ayyukan masana’antun shirya fina-finai da bidiyo na Najeriya. Hukumar na aiki da dokokin dake shafar tsaftace harkar fina-finai da bidiyo, koda fina-finan ba cikin gida ne ba ko kuma na kasashen ketare, kuma ita ce ke da alhakin kula da rejistar kamfanonin shirya fina-finai da bidiyo a fadin kasar.

NFVCB ta ce, tana farin ciki game da sakamakon yadda masana’antar ta fara samun nasarori tun a farkon shekarar bana, bisa lura da samun karuwar fina-finan da aka gabatarwa hukumar domin tantance su da kuma amincewa dasu a rubu’in farko na bana.

Hukumar tace fina-fian ta lura cewa, masana’antar Nollywood, ta kasance gagarumin bangaren dake bayar da gudunmawa ga bunkasar tattalin azrikin kasar.

Ta cigaba da cewa, fina-finai da ake samarwa sun nuna yadda fannin ke samar da guraben ayyukan yi na kai tsaye da wadanda ba na kai tsaye ba.(Ahmad)