logo

HAUSA

Kamaru da FAO sun sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru 5 don inganta samar da abinci mai gina jiki

2022-04-23 17:02:45 CMG Hausa

Hukumar samar da abinci da inganta aikin gona ta MDD (FAO), ta sanya hannu kan wani shiri na CPF tare da jamhuriyar Kamaru, wanda zai inganta aikin noma, da samar da abinci, da abinci mai gina jiki da kuma gudanar da albarkatun kasa a kasar ta tsakiyar Afrika na shekaru biyar masu zuwa.

An gudanar da bikin sanya hannun ne a babban birnin kasar Yaounde, tsakanin wakilin FAO dake kasar, Athman Mravili, da ministan ayyukan gona da bunkasa karkara, Gabriel Mbairobe.

Mbairobe ya bayyanawa manema labarai cewa, daftarin shirin yana kunshe da bangarori hudu. Na farko, yadda za a inganta ayyukan gona don samar da arziki ga kasar, na biyu, ya shafi batun yaki da matsalar sauyin yanayi, na uku, karfafa manufofin gwamnati domin cimma muradin samar da dawwamamman cigaba da nufin kawar da talauci da yaki da yunwa a kasar. Ya ce shirin zai gudana ne tsakanin shekarar 2022 zuwa 2026.

Za a aiwatar da shirin na CPF tsakanin gwamnatin Kamaru da hukumar FAO, tare da goyon bayan manyan masu ruwa da tsaki daga bangarori masu zaman kansu, da wasu hukumomin gwamnati, da kuma kungiyoyin fararen hula.(Ahmad)