logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya bada umarnin gaggauta ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa

2022-04-22 14:03:25 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya baiwa hukumomin tsaron kasar umarnin su kara himma domin kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a harin da ’yan bindiga suka kaddamar kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Babban mashawarci ga shugaban kasar a fannin tsaro, Babagana Monguno ya bayyanawa manema labarai cewa, shugaba Buhari ya bada umarnin ne a wajen taron majalisar tsaro ta kasar wanda shugaban kasar ya jagoranta a Abuja, babban birnin kasar.

Tun da farko dai, hukumar kula da sufurin jiragen kasan Najeriya ta sanar cewa, jirgin kasan na dauke da fasinjoji 362 da ma’aikata 20 a lokacin faruwar lamarin. Sannan jirgin yana dauke da taragu 14 a lokacin da maharan suka afkawa jirgin kasan.

Monguno ya bayyana cewa, shugaban Najeriyar ya bayyana lamarin da cewa ba zai sake faruwa ba a nan gaba, yayin da kasar mafi yawan al’umma a Afrika ke fama da kalubalolin tsaro.

Mai baiwa shugaban kasar shawara a harkar tsaron ya ce, rashin wadatattun fasahohi da karancin kwararru, na daga cikin dalilan dake haifar da kalubalolin da ake cigaba da samu na hare-haren ’yan ta’adda da na ’yan bindiga a Najeriya. (Ahmad)