logo

HAUSA

Mahukuntan Mali sun sanar da shirin mika mulki nan da watanni 24

2022-04-22 20:22:26 CMG Hausa

Firaministan gwamnatin rikon kwarya a kasar Mali Choguel Maiga, ya sanar da shirin mika mulki ga zababbiyar gwamnati a kasar, nan da watanni 24 masu zuwa.

Maiga, wanda ya sanar da hakan a birnin Bamako, fadar mulkin kasar, ya ce cikin wa’adin lokacin, za a gudanar da dukkanin shirya shiryen gudanar da babban zaben kasar mai inganci, wanda kowa zai aminta da shi.  (Saminu)