logo

HAUSA

Nijeriya Za Ta Buga Wasan Sada Zumunci Da Kasar Ecuador

2022-04-21 15:34:10 CMG HAUSA



Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya NFF da takwararta ta Kasar Ecuador a ranar Juma’a sun sanar da cewa tawagar kasashen biyu za su buga wasan sada zumunci a birnin New Jersey na kasar Amurka a ranar Alhamis 2 ga watan Yuni 2022.

Kungiyoyin biyu za su fafata a filin wasa na Red Bull Arena mai cin Mutum 25,000 a Harrison, New Jersey – filin wasan Kungiyar kwallon kafa ta Red Bulls. An bude filin wasan ne a watan Maris din shekarar 2010.

Ecuador, wacce a halin yanzu take matsayi na 46 a hukumar kwallon kafa ta duniya, ta kai zagaye na 16 a gasar cin kofin duniya ta FIFA a shekarar 2006 a Jamus.

Nijeriya dai ta halarci gasar cin kofin duniya ta FIFA sau shida, inda ta kai zagaye na 16 a 1994 da 1998 da kuma 2014.

 

 

Yadda Tauraruwar Benzema Take Ci Gaba Da Haskawa Tun Bayan Tafiyar Ronaldo

Dan wasa Karim Benzema ne ya ja ragamar Real Madrid a wasa na biyu da Chelsea karawar kwata fainal a Champions League ranar Talata kuma dan wasan shi ne ya zura kwallon da ta ba wa Real Madrid damar doke Chelsea.

Dan wasan tawagar Faransa shi ne ya ci Chelsea kwallo uku rigis a fafatawar da suka tashi 3-1 a Stamford Bridge ranar Laraba 6 ga Afirilu, kuma karo na biyu da ya ci kwallo uku rigis a bana a Champions League, bayan da ya ci Paris St Germain a zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.

Tsohon dan wasan na Lyon Benzema na kan ganiya sai cin kwallaye yake son ransa a kakar nan, duk da matsalar da ke gabansa zai daukaka kara ta cin amana, bayan da wata kotu ta same shi da laifi a Nuwamban bara.

 

Ana Bincike Kan Ronaldo, Bayan Ya Fasa Wayar Magoyin Bayan Everton

‘Yan Sandan birnin Merseyside na bincikar dan kwallon Manchester United, Cristiano Ronaldo, wanda ake zargi ya fasa wayar dan kallo bayan bullar wani bidiyo da yake yawo a kafar sada zumunta dauke da sako, ya nuna lokacin da ya kwada wayar da kasa, bayan da Manchester United ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Everton a ran-ar Asabar din da ta gabata.

Sai dai daga baya Ronaldo mai shekara 37 a duniya ya nemi afuwa a kafar sada zu-munta kuma ya bayyana cewa zai gayyaci matashin magoyin bayan domin ya zo ya kalli wasan Manchester United a filin wasa na Old Trafford. ”Ina son na nemi afuwa kan fusata da na yi, kuma idan da hali, zan so na gayyaci magoyin bayan domin ya kalli wasa a Old Trafforrd,” kamar yadda Ronaldo, wanda ya koma Manchester United a farkon wannan kakar ya rubuta a shafinsa na sada zumunta.

‘Yan Sandan birnin Merseside sun ce suna binciken rahoto kan zargin cin zarafi’ da aka yi a filin wasa na Goodison Park ranar Asabar kuma jami’in da ke magana da yawun jami’an tsaro ya ce suna tattaunawa da Manchester United da kuma Everton kan lamarin.

”A lokacin da ‘yan wasan ke barin fili da misalin karfe 2.30, an yi rahoton cewar an ci zarafin wani yaro daga wajen wani dan wasa baki a lokacin da za su bar filin kuma ana kan bincike kuma jami’ai na aiki tare da mahukuntan Everton da neman faifan bidiyon da aka nadi lamarin da ganawa da shaidu, domin tabbatar da hujjar abin da ya faru.” In ji. ‘yan sandan birnin

Suka ci gaba da cewa ”Ana neman duk wanda yake da shaidar kan abin da ya faru da ya tuntubi ‘yan Sandan Merseyside a kafar sada zumunta a Twitter MerPolCC ko kuma ta Facebook Merseyside Police, sai a tuntuba ta binciken da aka yi wa lamba 228 na ranar 9 ga watan Afirilun 2022.”

Ita ma kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta ce ta san da zargin da ake yi sannan za ta bayar da hadin kai kan binciken da ‘yan Sanda ke yi. Bayan da aka ci United hakan ya kawo mata cikas kan neman gurbin shiga Champions League a badi, bayan da Everton ke fatan kaucewa daga faduwa daga Premier League ta bana.

Sai dai Ronaldo dan kwallon tawagar Portugal ya ce yana da wahala ka boye fushinka a irin halin da suke ciki ko da yake dole suke martabawa da hakuri, da kuma yin halayya ta gari da yara za su kwaikwaiya masu sha’awar kwallon kafa.

 

 

Za A Yi Gwanjon Rigar Maradona Fam Miliyan Hudu

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa rigar da Diego Maradona ya saka a lokacin da ya zura kwallo a ragar Ingila ta hanyar amfani hannunsa a gasar cin kofin duniya ta shekarar 1986, ana sa ran za a sayar da ita a kan akalla fam miliyan hudu.

Rigar dai a yanzu mallakin tsohon dan wasan tsakiya ce na Ingila Stebe Hodge, wan-da ya yi musayar riga da Maradona bayan da Argentina ta doke su da ci 2-1 a gasar cin kofin duniya a shekara ta 1986. A kimanin shekaru biyu da suka gabata, bayan mutu-war Maradona a shekara ta 2020, tsohon dan wasa Hodge ya ce rigar gwarzon dan wasan ba ta sayarwa ba ce sai dai ana ganin a halin yanzu kamar ya canja shawara.

Maradona, wanda ya jagoranci Argentina zuwa nasarar lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 1986, na daga cikin manyan gwarazan ‘yan wasa a tarihin kwallon kafa, ya mutu yana da shekaru 60 sakamakon bugun zuciya.

A tarihi dai rigar da gwarzon duniya na kasar Brazil Pele ya sanya a wasan karshe na gasar cin kofin duniya a shekarar 1970 ita ce rigar kwallon kafa mafi tsada da aka sayar da ita a gwanjo, a cewar littafin adana ababen tarihi na duniya wato ‘Guinness World Records’.

Kuma kamar yadda rahotanni suka bayyana an yi gwanjon rigar ta Pele ne a kan kudi fam miliyan 157 da dubu 750 a shekarar 2002, lokacin da kasar ta Brazil ta lashe kofin duniya karo na biyar a kasashen Korea da Japan..