logo

HAUSA

Jirgin saman Najeriya ya yi hatsari tare da kashe matuka 2

2022-04-21 11:14:30 CMG HAUSA

 Mai magana da yawun rundunar sojin saman Najeriya, Erward Gabkwet ya bayyana a jiya Laraba cewa, wani jirgin sama na sojojin saman Najeriya ya yi hatsari a arewacin jihar Kaduna, tare da halaka matukansa biyu.

Wata sanarwar da jami’in ya fitar ta bayyana cewa, an fara gudanar da bincike kan hatsarin jirgin na Super Mushshak da sojojin ke amfani da shi wajen samun horo, wanda ya afku a sansanin sojojin sama da ke Kaduna.

Gabkwet ya ce, abin takaici hatsarin jirgin na jiya, wata matashiya ne da ke nuna irin hadarin dake tattare da sana’ar tukin jiragen soja da kuma kasadar da matukan jiragen sojin saman Najeriya NAF ke ci gaba da fuskanta a kullum, a kokarin kare martabar yankunan Najeriya.

Hatsari mafi girma na karshe da wani jirgin saman sojojin Najeriyar ya yi, shi ne wanda ya faru a kusa da filin jirgin sama na kasa da kasa dake Kaduna a watan Mayun shekarar 2021, inda ya halaka dukkan jami'an soji 11 da ke cikin jirgin, ciki har da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Ibrahim Attahiru. (Ibrahim)