logo

HAUSA

Mahangar Xi Jinping Game Da Babbar Manufar Jagoranci

2022-04-21 16:36:47 CMG Hausa

A tsawon shakaru masu yawa, masana da kwararru, da masu dinbin basira a sassan rayuwa daban daban na kasar Sin, sun sha tattaunawa game da ainihin babbar manufar jagorancin kasa, ko abu mafi muhimminci ga kowace irin kasa. Daga karshe dai, a kan rinjayar da ginshikai kamar tsaro, da managarcin tsarin siyasa, ko kuma gogewar jami’an dake jagorantar sassan hukumomi.

To amma ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, amsar ita ce, sanya al’ummar kasa cikin yanayi na farin ciki. Hakan ne ma ya sa, a yayin da yake ziyarar aiki a lardunan kasar Sin, ya kan ziyarci gidajen talakawa a yankunan karkara domin sanin halin da suke ciki.

Ga misali, a shekarar 2013, shugaba Xi ya ziyarci kauyen ’yan kabilar Miao dake sassan tsaunukan lardin Hunan. A wancan lokaci ya shiga gidajen talakawa, inda ya bukaci sanin irin nau’o’in abinci da ’ya’yan itatuwa da suke iya samu domin rayuwa.

A lokacin da yake matashi, Xi ya shafe tsawon shekaru 7 a kauyen Liangjiahe na lardin Shaanxi, wurin da a lokacin kauye ne maras wadata. Bayan ganewa idanunsa halin kunci da al’ummu mazauna yankunan tsaunuka ke rayuwa a ciki, shugaban na Sin, ya kuduri aniyar bautawa jama’a, da tabbatar da rayuwar su ta kyautata.

Ya kuma cimma wannan buri, ta hanyar zaburar da daukacin sassan jagororin kasar, game da bukatar sanya jin dadin jama’a gaban komai.

Ko shakka babu, wannan kwazo na shugaba Xi ya haifar da ‘da mai ido, domin kuwa, a yayin wata ziyara da ya kai kauyen Wang Deli dake yankin tsaunukan lardin Guangxi a bazarar shekarar 2021, ya zanta da wani magidanci, wanda ya ce masa "Shugaba kana shan aiki, amma duk da haka ka yi kokarin ziyartar mu. Muna matukar godiya".

Da jin haka sai shugaba Xi ya ce masa "To ai wannan ne aikin da na sanya gaba." A mahangar shugaba Xi, sanya al’umma farin ciki shi ne babban aikin duk wani shugaba.

Ko shakka babu, wannan manufa ce mai cikakkiyar ma’ana. Domin kuwa ba wata al’umma da ba ta fatan yin rayuwa cikin farin ciki! (Saminu Hassan)