logo

HAUSA

Asiya da duniya baki daya na bukatar tsarin gudanar da tsaro na duniya

2022-04-21 20:24:32 CMG Hausa

Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping, ke gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, a taron dandalin kasashen Asiya na Boao a Alhamis din nan, ya ce kafin din wani ci gaba, dole ne a samar da tsaro, duba da cewa daukacin bil adama, na rayuwa ne dunkule karkashin al’umma mai tsaro.

Shugaban na Sin ya ce, shawarar samar da tsarin tabbatar da tsaron kasa da kasa, kari ne kan abubuwan da Sin ke bayarwa gudummawa ga duniya, wanda ke kunshe da hangen nesan Sinawa, mai tafiya kafada da kafada da sauye sauyen da duniya ke fuskanta, a kan lokaci kuma daidai da tarihi. Ya ce yankin Asiya da duniya baki daya, na bukatar wannan tsari na tsaron duniya. (Saminu)