logo

HAUSA

Tsohon gwamnan jihar California: Ya kamata Amurka ta amince da bambance-bambancen dake tsakaninta da Sin da yin watsi da tunanin caccar baki

2022-04-21 15:30:57 CMG HAUSA

 

Tsohon gwamnan jihar California ta kasar Amurka Jerry Brown, ya wallafa wani bayani a mujallar NYRB ta Amurka mai taken “Mahaukacin ra’ayi na Washington”, inda ya nuna cewa, tunanin da wasu ’yan siyasar Amurka ke yi kan wani bangare ya samu riba kana wani bangare ya yi hasara, ya saba hakikanin halin da bangarorin biyu suke ciki na bukatar juna da yin takara don samun ci gaba tare. A cewarsa, ya kamata Amurka ta amince da bambance-bambancen dake tsakaninsu, tunanin rashin hankali da ’yan siyasa suke yi zai jefa kasar cikin mawuyacin hali.

Rahotanni na cewa, wasu mutane kamar tsohon mataimakin sakataren ma’aikatar tsaron kasar, kana direktan kula da harkokin kasar Sin na kwamitin tsaron kasar Amurka Rush Doshi da wasu ’yan siyasa, na ci gaba da yada jita-jita wai za a tada rigingimu tsakanin kasashe mafiya karfi, abin da suke mayar da hankali shi ne hana Sin zama jigo a nahiyar Asiya da ma duniya. A hakika, wannan wata hujja ce ta tada wani yaki da wasu ’yan siyasa ke yi a wajen nahiyar Amurka.

Sai dai Jerry Brown ya yi imanin cewa, ko da yake ba za a iya magance takara tsakanin Amurka da Sin ba, amma bangaroin biyu suna da moriya iri daya, kuma kasa ita kadai ba za ta magance matsalar rage fitar da hayaki mai dumama yanayin duniya da makaman nukiliya da yaduwar annoba da sabbin fasahohi masu kawo tarnaki ga duniya ba. Duniya na matukar bukatar hadin gwiwar kasa da kasa. Ko da yake kasashen Sin da Amurka na da bambancin tsarin mulkin kasa, amma akwai bukatar kasashen da su koyi zama tare cikin lumana, da yin hadin gwiwa a maimakon tada sabon yakin cacar baka. (Amina Xu)