logo

HAUSA

An bude taron nahiyar Afrika na farko kan gora da iccen Rattan a Kamaru

2022-04-21 11:13:11 CMG HAUSA

 

An bude taron nahiyar Afrika na farko kan gora da iccen Rattan a birnin Yaounden Kamaru a jiya Laraba, domin tattauna yadda gorar da iccen Rattan, za su bayar da gudunmuwa ga ci gaba mai dorewa.

Gwamnatin Kamaru ce ta shirya taron na yini 3 da hadin gwiwar kungiyar dake rajin amfani da gora da rattan wajen kyautata muhalli ta kasa da kasa (INBAR).

Daraktan kungiyar INBAR a yankin tsakiyar Afrika Rene Kaam, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a farkon taron cewa, gora da rattan na samawar kasashe da abokan hulda dimbin mafita ga matsalar sauyin yanayi. Ya ce idan aka fara daukarsu a matsayin albarkatu masu muhimmanci a cikin dabarun kasa da shirye-shiryen duniya, to za su rage mummunan tasirin nau’ikan sauyin yanayi kan miliyoyin yankunan karkara.

INBAR, kungiya ce mai zaman kanta da aka kafa a shekarar 1997, dake rajin amfani da gora da rattan don samun ci gaba mai dorewa ta hanyar kyautata muhalli. Yanzu haka, ta kunshi kasashe mambobi 48, ciki har da kasashen Afrika 20. (Fa’iza Mustapha)