logo

HAUSA

Gudummawar da dakarun tabbatar da zaman lafiya na kasar Sin suka bayar a sassan duniya cikin shekaru 30

2022-04-20 08:42:48 CMG Hausa

A bana ne rukunin sojojin wanzar da zaman lafiya da kasar Sin ta kafa, ke cika shekaru 30 da shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya karkashin laimar MDD.

A shekarar 1990 ne kasar Sin ta tura dakarun sanya-ido ga MDD, matakin dake zama mafarin shigar dakarun na kasar Sin ayyukan tabbatar da zaman lafiya a sassan duniya. A ranar 16 ga watan Afrilun shekarar 1992, kasar Sin ta tura rukunin farko na dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa kasar Cambodiya.


Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta tura rukunonin sojojin tabbatar da zaman lafiya dubu 50 zuwa ayyukan tabbatar da zaman lafiya 25 a sama da kasashe da yankuna 20 na duniya. Dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Sin, sun samar da zaman lafiya da tsaro gami da fata mai kyau, a rayuwar al’ummomin yankunan dake fama da yake-yake da aka tura su.

A shekarar 2013, kasar Sin ta tura tawagogin tabbatar da zaman lafiya guda 9, zuwa kasar Mali, inda suka gudanar da ayyukan sintiri, bayar da rakiya, ayyukan da suka samar musu da yabo matuka.


A sama da shekaru 16 da dakarun wanzar da zaman lafiyar Sin suka shafe suna gudanar da ayyukansu a kasar Lebanon, dakarun na Sin sun kammala ayyukansu cikin nasara, kamar kawar da nakiyoyi da aka binne a karkashin kasa, da aikin injiniya da gyare-gyaren kayan aiki da samar da hidimomi na lafiya da ayyukan jin kai.

Baya ga gudummawar tabbatar da zaman lafiya a kasashe da yankunan duniya, kasar Sin ta zama kasa ta biyu mafi bayar da gudummawa ga ayyukan tabbatar da zaman lafiya na MDD. Kana kasa mai bayar da kudadenta na karo-karo a kan lokaci, cikin kasashe biyar masu kujerun din-din-din a kwamitin sulhu na MDD. Wannan ya kara tabbatar da cewa, kasar Sin ta kasance a kan gaba wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya da daidaito a harkokin kasa da kasa. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)