logo

HAUSA

Ana neman iznin shigar da layin da ya ratsa tsakiyar birnin Beijing cikin jerin kayayyakin tarihi na duniya a fannin al’adu da aka gada daga kaka da kakanni

2022-04-20 15:23:09 CMG Hausa


Layin da ya ratsa tsakiyar birnin Beijing, ya fara ne daga hasumiyar kararrawa da ginin adana babbar ganga dake arewacin birnin, har zuwa babbar kofar Yong Ding dake kudancin birnin, kuma gaba daya, tsawonsa ya kai kilomita 7.8. A kan wannan layi, akwai wuraren tarihi da dama wadanda suke bayyana al’adu da tarihin birnin Beijing masu muhimmanci. A halin yanzu, an gabatar da bukatar neman shigar da layin da ya ratsa tsakiyar birnin Beijing, cikin jerin kayayyakin tarihi a fannin al’adu na duniya da aka gada daga kaka da kakanni. (Maryam)