logo

HAUSA

Ba A Sauyawa Tuwo Suna

2022-04-20 18:33:52 CMG Hausa

Sanin kowa ne cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, ita ce kadai halastacciyar gwamnati dake wakiltar kasar Sin. Haka kuma kasancewar kasar Sin daya tilo a duniya, ita ce babbar manufar da kasashen duniya suka amince da ita, kana tushen siyasa na raya hulda tsakanin Sin da duk kasashen da suka kulla ko ma suke son kulla alaka da kasar Sin.

Yanzu haka akwai kasashe 180 a duniya, wadanda suka amince tare da goyon bayan manufar kasar Sin daya tilo a duniya, kuma wannan ita ce yarjejeniya ta zahiri da kasashen duniya suka amince da ita.

Kasar Amurka na daga cikin kasashen da suka amince da wannan manufa, baya ga sanarwoyi uku da kasashen biyu suka aminta da su a kan alakar dake tsakaninsu, amma har yanzu Amurka ta yi biris tare da neman lalata tushen siyasa na huldar dake tsakaninta da kasar Sin, inda take ci gaba da hulda da yankin Taiwan na kasar Sin.

Sanin kowa ne cewa, Taiwan ba kasa ba ce, wani bangare ne na kasar Sin. Duk abun da ’yan aware suke yi na jirkita gaskiya, ko kadan ba zai taba canja gaskiyar lamarin ba, wato babban yanki da kuma yankin Taiwan duka suna karkashin ikon Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin ne.

A baya-bayan ne, wasu ’yan majalisun dokokin Amurkar suka ziyarci yankin, abin da masu fashin baki suka bayyana a matsayin wani salo na takala da gangan, da take ka’idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya da kuma tanadin sanarwoyin hadin gwiwa guda 3 da Sin da Amurka suka fitar. Ziyarar da bangaren na Sin ya yi Allah wadai da ita.

Masu fashin baki na cewa, ziyarar jami’an na Amurka munafurci ne da nuna rashin gaskiya, domin a baya Amurka ta ce ba ta goyon bayan ’yancin kan Taiwan, a daya bangaren kuma, tana aikewa da wani mummunan sako ga masu rajin ballewa. Kuma kasar Sin tana adawa da hakan.

A kokarin da kasar Sin ke yi na kara fahimtar da kasashen duniya game da manufar kasar Sin daya tak a duniya, sanarwar da aka fitar bayan kammala cikakken zaman karo na shida na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19, ta bayyana karara cewa, kasar Sin za ta ci gaba da martaba ka'idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da kuma matsaya irin wannan da aka cimma a shekarar 1992, wadda ke adawa da ayyukan ’yan aware dake neman ’yancin kai na Taiwan, da tsoma baki daga waje.

Wannan ya kara fayyace tsayin daka na kasar Sin, da kuma matsayinta na kare ikon mallakar kasa da cikakken yankunanta, har ma da tsaro da moriyar ci gabanta baki daya. Ta kuma sha alwashin dakile duk wani kutse daga waje da masu neman ’yancin kan Taiwan. Kuma duk wanda bai ji gari ba, to zai ji Hoho.

Kasar Sin na kara jaddada cewa, duk kasar dake son kulla huldar diflomasiya da kasar Sin, waijibi ne ta martaba wannan manufa. Wato Kasar Sin daya ce tak a duniya, Ma’ana ita ce Ba a Sauyawa Tuwo Suna. (Ibrahim Yaya)