logo

HAUSA

Bikin Easter da ke cike da harbe-harben bindiga

2022-04-20 20:14:58 CMG Hausa

A karshen makon da ya gabata, munanan harbe-harben bindiga da aka samu a sassan kasar Amurka, sun hallaka mutane tare da jikkata wasu da dama, wadanda suka girgiza al’ummar kasar da ke bikin Easter.

A birnin Pittsburgh na jihar Pennsylvania, harbe-harben bindiga sun hallaka mutane biyu tare da jikkata wasu a kalla 8. A Hampton, South Carolina, wasu mutane 9 sun ji raunuka sakamakon harbe-harben bindiga, a yayin da a birnin Columbia, babban birnin jihar, harbe-harben bindiga da aka yi a wani kanti ya jikkata wasu mutane 14. Sai kuma a birnin Syracuse na jihar New York, harbe-harben bindiga da aka yi sun yi sanadiyyar mutuwar mutum guda, tare da ji wa wasu 4 raunuka.

Alkaluman da aka samar sun yi nuni da cewa, daga farkon bana zuwa ranar 17 ga wata, mutane 12,502 sun rasa rayukansu a sakamakon harbe-harben bindiga a kasar Amurka, a yayin da wasu 10,024 suka ji raunuka.

Shin ba kasar Amurka ce ke daukar kanta a matsayin abin koyi wajen kare hakkin bil Adam ba? Me ya hana gwamnatin kasar ta dauki matakai na shawo kan matsalolin harbe-harben bindiga a kasar? Me ya sa ake matukar shan wahala wajen aikin kayyade mallakar bindigogi a kasar? (Mai zane:Mustapha Bulama)