logo

HAUSA

Sin da kasashe makwabtanta na karfafa huldarsu don rungumar makomar bai daya

2022-04-20 14:18:22 CMG Hausa

Daga shekarar 2013, bisa tsarin diflomasiya na “sada zumunta da makwabta”, kasar Sin ta yi ta bunkasa huldar da ke tsakaninta da kasashe makwabtanta, tare da gina wata al’umma mai kyakkyawar makoma tare da kasashen dake makwabataka da ita.

“Kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen zama lafiya da kasashe makwabtanta da kuma sada zumunta da su, tare da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna a tsakaninsu, ta yadda kasashe makwabtanmu za su ci gajiyar ci gabanmu.”

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fadi haka ne a watan Afrilun shekarar 2013, a yayin da ya gabatar da jawabi a gun taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar harkokin Asiya na Boao, inda ya bayyana ra’ayinsa game da hadin gwiwar shiyyoyi, furucin da ya karyata jita-jitar da ake bazawa wai “Sin barazana ce”.

Har kullum kasar Sin na zama lafiya da kasashe makwabtanta, kuma tana kokarin sada zumunta da su da kuma amfana da ci gaban da ta samu. A ranar 3 ga watan Disamban bara ne, aka kaddamar da layin dogo a tsakanin Sin da Laos, abin da ya yi matukar burge firaministan kasar ta Laos Phankham Viphavanh, wanda a lokacin ya shiga jirgin mai suna Lancang da ya fara zirga-zirga a kan layin a karo na farko, ya ce,“Na yi matukar farin ciki hawa jirgin. Wannan layin dogo ya shaida yadda kasar Laos ta fara zamanintar da harkokin zirga-zirga wadanda a baya suka dogara ga hanyoyin mota. Wannan layin dogo zai taimaka ga bunkasa tattalin arziki da rayuwar al’umma dake kasarmu, kana zai hade kasar Sin da kasashen ASEAN da kuma Laos da sauran kasashen yankin, kuma hakan zai haifar da moriya gare mu.”

A yayin da take aiwatar da hadin gwiwa da kasashe makwabtanta, kullum kasar Sin tana martaba manufar cin moriyar juna, wadda take kokarin samar da damammakin ci gaba ga kasashe makwabtanta. (Lubabatu)