logo

HAUSA

Kila shan taba da masu ciki suka yi zai kara barazanar haihuwar jarirai da ciwon zuciya

2022-04-19 11:28:25 CMG Hausa

 

Jami’ar Bristol ta kasar Birtaniya ta gabatar da wani sakamakon nazari a kwanan baya, inda ta nuna cewa, idan mata su ka sha taba yayin da suke da ciki, to, watakila za su haifi ‘ya’yansu da ciwon zuciya.

Tawagar masanan kasa da kasa karkashin shugabancin jami’ar Bristol ta tantance kan bayanan da suka shafi iyalai fiye da dubu 230 daga wasu kasashen Turai dangane da haihuwa da lafiya. Masu nazarin sun kwatanta illolin da wasu batutuwa suka haifar kan barazanar haihuwar ‘ya’ya da ciwon zuciya. Wadannan batutuwan da suka shafi mahaifa mata sun hada da mizanin BMI, al’adar shan taba, yawan giyar da su kan sha, da dai sauransu. Mizanin BMI, mizani ne na awon nauyin mutum a kilogiram a raba da tsayin mutum a mita sikwaya.

Sakamakon nazarin ya shaida cewa, idan masu juna biyu su ka sha taba, to, akwai yiwuwar za su haifi ‘ya’yansu da ciwon zuciya. Amma fama da matsalar kiba, ko kuma shan giya a lokacin samun ciki, ba muhimman dalilan da sukan sa ahaifi ‘ya’ya da ciwon zuciya ba ne.

Masu nazarin sun ba da shawarar cewa, kamata ya yi matan da suka cancanci haihuwa su dakatar da shan taba. Kuma dukkan mahaifa maza da mata wajibi ne su kiyaye daidaiton nauyin jiki da sanya ka’ida kan yawan giyar da sukan sha kafin samun ciki da kuma lokacin samun ciki.

Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, wata likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, sakamakon nazarin ya kara nuna mana cewa, ana bukatar kara nuna goyon baya kan dakatar da shan taba a duk fadin duniya. Nan gaba idan aka kara fahimtar yadda shan taba a lokacin rainon ciki zai kara barazanar haihuwar ‘ya’ya da ciwon zuciya, to, zai taimaka wajen fito da sabuwar dabarar rigakafin ciwon. (Tasallah Yuan)