logo

HAUSA

Rubu’i na farkon bana: al’ummar Sin sun ci gaba da samun karuwar kudin shiga

2022-04-19 11:23:32 CMG Hausa

 

A rubu’i na farko na shekarar 2022 da muke ciki, yawan kudin shigar al’ummar kasar Sin yana ci gaba da karuwa. Alkaluman da hukumar kididdihar kasar Sin ta fitar a jiya ya nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Maris, matsakaicin yawan kudin shigar ko wane Basine, ya kai kudin Sin RMB yuan 10345, wanda ya karu da kaso 6.3% bisa makamancin lokaci na shekarar 2021. (Tasallah Yuan)