logo

HAUSA

Zimbabwe za ta fara amfani da tsarin ba da ilimin firamare kyauta daga shekarar 2023

2022-04-19 11:18:02 CMG HAUSA

 

            

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya sanar a jiya Litinin cewa, kasarsa za ta fara aiwatar da tsarin ba da ilmin firamare kyauta daga shekara mai zuwa, a wani bangare na kokarin da gwamnati ke yi na tabbatar da ganin an samar da ilimi ga kowa.

Mnangagwa ya bayyana hakan ne, yayin jawabin da ya gabatar ga ’yan kasa a Bulawayo, birni na biyu mafi girma na kasar, albarkacin bukukuwan samun ’yanci, don murnar cika shekaru 42 da kasar ta samu ’yancin siyasa.

Bugu da kari, Mnangagwa ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta koyar da darussan kimiya da fasarar kere-kere da Lissafi (STEM) a makarantu.

Shugaba Mnangagwa ya kara da cewa, idan aka yi la’akari da cewa, matakin ci gaban al’umma ya dogara ne da koyarwa da kuma karbuwar kimiyya, da fasaha da kirkire-kirkire, to za a ci gaba da yin amfani da albarkatu, wajen fadada koyar da ilimin kimiyya da ababen more rayuwa a dukkan makarantu da cibiyoyi da ke fadin kasar. (Ibrahim)