Me Ya Haifar Da Tagomashin Tattalin Arzikin Sin Duk Da Fama Da Annobar COVID-19?
2022-04-18 18:48:43 CMG Hausa
Masu hikimar magana cewa, “dabara ba ta daure kaya, sai an hada da igiya.” Sannan a wani kaulin a kan ce, “tun ran gini tun zane.” Tun bayan da aka samu barkewar annobar COVID-19 sama da shekaru biyu da suka gabata, wacce ta zama tamkar ruwan dare gama duniya, tattalin arzikin kasashen duniya ya shiga cikin yanayin rashin tabbas, sakamakon daukar wasu matakai na dakile annobar wadanda ke da alaka ta kut-da-kut da tattalin arzikin, misali kamar dokokin kulle da kasashen duniya suka sanya sun taka rawa matuka wajen yin gabala kan cutar. Ko da yake, matakan sun haifar da babban gibi ga tattalin arzikin duniya duk da cewa daukar matakan batu ne wanda ba zai yiwu a iya kauce musu ba. Sai dai wani abin sha’awa shi ne, irin matakan da kasar Sin ta dauka a karon farko tun bayan bullar annobar, sun yi tasiri matuka wajen kafa kyakkyawan tubalin bunkasar tattalin arzikin kasar. Hakika, tun daga farkon shekarar 2020 zuwa 2021, alkaluman da hukumomi ke fitarwa game da yanayin tattalin arzikin kasar suna kara faranta. Alal misali, bayanai na baya bayan nan da hukumar kididdigar kasar Sin wato (NBS) ta bayyana sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar ya kama hanyar bunkasa a rubu’i na farkon shekarar 2022 da muke ciki, duk da kalubalen da ake fuskanta daga yanayi mai sarkakiya da ke karuwa a duniya, gami da sake bullar cutar COVID-19 a cikin gida. Alkaluman hukumar kididdigar na nuna cewa, GDPn kasar ya karu da kashi 4.8 cikin dari a kowace shekara a cikin watannin ukun farko, inda ya karu da kashi 4 cikin dari a rubu'i na hudu na bara. Kakakin hukumar NBS na kasar Sin ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar, yana gudana yadda ya kamata tare da ci gaba da farfadowa, yayin da kasar ta yi nasarar daidaita matakan yaki da COVID-19, da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Ko da yake, hanyoyin da kasar ke bi wajen farfado da tattalin arzikin ya kunshi matakan kyautata hada-hadar cinikayya a tsakaninta da kasa da kasa. Misali, a karshen makon da ya gabata, an bude baje kolin hajojin da ake shigowa da wadanda ake fitarwa daga kasar Sin wanda aka fi sani da “Canton Fair” ta yanar gizo, sai dai bikin ya gudana ne cikin yanayi na yaki da annobar COVID-19. Baje kolin na kwanaki 10 a bana ya samu hallarar sama da masu baje hajoji na cikin gidan kasar Sin da na waje har 25,500. Masu baje kolin za su samu hidimomin yanar gizo daban daban, kamar nuna hajoji ta yanar gizo, da musayar damar kasuwanci, da kuma kaddamar da hajoji. Kamfanoni mahalarta sun gabatar da hajojin tallatawa sama da miliyan 2.9, ciki har da wasu sabbin hajoji sama da 900,000, da hajoji marasa gurbata muhalli sama da 480,000, kuma bayanai sun nuna cewa, nau’o’in hajojin sun kasance mafiya yawa da aka taba bajewa a baje kolin da suka gabata. An yi kiyasin cewa, yawan kudin cinikin kayayyaki da aka samu a kasar Sin a shekarar 2021 ya zarce dalar Amurka triliyan 6. Ko shakka babu, tagomashin da tattalin arzikin kasar Sin ya samu ba kawai zai amfanawa kasar kadai ba ne, har ma ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da cinikayyar duniya. (Ahmad Fagam)