Duk da fuskantar kalubale tattalin arzikin Sin ya ci gaba da daidaita
2022-04-18 21:09:18 CMG Hausa
Alkaluma daga hukumar dake lura da tattalin arzikin kasar Sin, sun nuna cewa, cikin rubu’in farko na shekarar nan ta 2022, ma’aunin GDPn kasar ya kai kudin Sin yuan biliyan 27,017.8, adadin da ya nuna karuwar kaso 4.8 bisa dari a shekara guda.
Duk da fuskantar kalubale da dama, tattalin arzikin Sin ya ci gaba da bunkasa, tare da samun daidaito a matakin ayyukan masana’antu na kasa da kasa cikin kyakkyawan yanayi.
Bisa jimilla, tattalin arzikin Sin ya ci gaba da farfadowa, da samun ci gaba a rubu’in na farko, inda alkaluman gudanarsa, suka nuna yana habaka bisa inganci, kuma sannu a hankali yana ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya. (Saminu)