logo

HAUSA

Likita Lu Shengmei: Sadaukar da rayuwarta wajen taimakawa mazauna yankunan karkara wajen inganta lafiyarsu

2022-04-18 14:01:04 CMG Hausa

Cikin shekaru 50 da suka gabata, Lu Shengmei, tsohuwar mataimakiyar shugaba kuma darakta a sashen kula da lafiyar yara na asibitin jama’a na gundumar Jia, ta sadaukar da rayuwarta wajen taimakawa mazauna wurin, wata gunduma dake birnin Yulin na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin, wajen inganta lafiyarsu. Sinawa da dama na mamakin yadda Lu Shengmei, wadda ta kammala karatu daga wata jami’a a Beijing ke mayar da hankali kan aikinta, take kuma jure rayuwar karkara a Yulin. Idan da za su ji labarin Lu, watakila za su iya fahimtar dalilin da ya sa take matukar son rayuwarta ta kauye da yadda ta samu kuzari, a matsayinta na mambar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, wajen cika alkawarin da ta dauka gomman shekaru da suka gabata, na ci gaba da kokarin taimakawa mazauna gundumar Jia kula da lafiyarsu.

A shekarar 1961, Lu Shengmei ta mika bukatar zama mambar JKS ga reshen jam’iyyar dake makarantarsu ta midil. A cikin bukatar, ta rubuta kamar haka, “zan sadaukar da duk wani kokarina ga yayata manufar jam’iyya cikin shekaru 50 masu zuwa.” Cikin wani rahoto da ta mikawa kungiyar jam’iyyar ta asibitin jim kadan bayan ta fara aiki, a gundumar Jia a watan Disamban 1968, Lu ta yi bayani game da ci gaban akidojinta. Ta kuma yi alkawarin ci gaba da kokarin taimakawa mazauna gundumar wajen inganta lafiyarsu cikin shekaru 50 daga sannan. Duk da irin wahalhalu da kalubalen da ta fuskanta, Lu ta yi namijin kokari wajen cika alkawarin da ta yi.

Duk da shigewar lokaci, Lu na iya tuna farin cikin da ta yi da ta samu labari a 1968 cewa, za ta yi aiki a gundumar Jia. A lokacin, tana gab da kammala karatu daga jami’ar ilmin likitanci ta Beijing. Lu ta ce, “Galibinmu, mun yi farin cikin samun labarin cewa, bayan mun kammala jami’a, za mu yi aiki a asibitoci ko cibiyoyin lafiya dake wurare masu nisa dake cikin yanayin maras kyau. Mun kuma kuduri niyyar jajircewa wajen ganin mun cimma burin da jam’iyya ke da shi a kan mu.”  

Sai da Lu ta isa gundumar Jia a watan Disamban 1968, sannan ta gano yadda yankin ke fama da koma bayan tattalin arziki. Gundumar Jia dake yankin tsaunikan Loess, wuri ne mai karancin ruwa. Lu ta yi mamakin ganin ginin asibitin a tsakanin koguna. Baya ga haka, a kan gadon da aka gina da kasa za ta kwanta, ga kuma cizo ko warin kudan cizo. Duk da haka, ba ta yi kasa a gwiwa ba saboda irin jajircewarta, inda cikin kankanin lokaci ta saba da sabon mazauninta.

Lu ta damu bayan ta gano cikin gajeren lokaci bayan isarta gundumar Jia cewa, mazauna yankin da dama ba su da ilimin kula da lafiya. Wannan ya ba ta kwarin gwiwar kara jajircewa kan aikinta na likita, wajen taimakawa mutanen ta fuskar wayar musu da kai game da kiwon lafiya.

Bisa la’akari da rashin wadataccen tsarin sufuri, yana wahala mutane masu fama da rashin lafiya mai tsanani su je asibiti. Don haka, likitoci ne ke zuwa gidajensu. Lu ba za ta taba manta yadda ta ji ba, lokacin da ta kai ziyara gidansu wani mara lafiya a ranar da ake fama da dusar kankara, inda ta tarar da ‘yan uwansa cikin damuwa. Ta fadi sau da dama yayin da take tafiya a yankin mai duwatsu. Saboda ziyarar da Lu ta kai a kan lokaci, yaron mai fama da ciwon limonia da kuma matsalar zuciya, ya samu sauki cikin wasu ‘yan kwanki. Lu da ta san yadda cututtuka ke saurin yaduwa, ba ta bata lokaci ba wajen ziyartar sauran iyalai a kauyen. Cikin gajeren lokaci, Lu ta bayar da kulawa ga sauran wasu yara 5.

Domin bayyana godiyarta ga Lu, daya daga cikin iyayen yaran ta ba ta takalma da aka yi da auduga. Matar na fatan Lu za ta samu saukin tafiya a hanyar mai tsaunika idan ta sanya takalman. A yayin da ta kalli matar, Lu ta fahimci bukata mai tsanani da ake da ita na likitoci a yankunan karkara.

Lu ta halarci wani kwas na horo tsakanin shekarar 1981 zuwa 1983 da asibitin Peking ya shirya. Manufar kwas din ita ce, taimakawa likitoci daga yankuna daban-daban na kasar Sin, inganta kwarewarsu. Bisa la’akari da hazakar Lu, da dama daga cikin takwarorinta sun bada shawarar a tura ta aiki a wani babban asibiti dake Beijing ko Xi’an, babban birnin lardin Shaanxi. Sai dai Lu, ta fi son ta ci gaba da aiki a gundumar Jia.

Jim kadan bayan komawarta gundumar Jia a shekarar 1983, Lu ta bada shawarar kafa sashen kula da lafiyar yara a asibitin jama’a na gundumar. Sai kuma aka ba ta mukamin daraktan sashen. A sannan, Lu ta kafa wata doka, wadda ta nemi likitoci a sashen su taimakawa marasa lafiya tsimin kudin da ake kashewa na kiwon lafiya. Haka kuma ta karfafawa likitocin gwiwar taimakawa marasa lafiya daga gidaje masu karamin karfi.

Cikin shekaru kalilan da kafa sashen, Lu ta samar da kudi, ta yadda nas nas dake aiki a sashen za su iya halarta kwasakwasan horo da asibitin yara na Xi’an ke samarwa. Kuma bisa basira da jajircewarsu, nan da ba a dade ba ma’aikatan jinyar suka goge kan aikinsu.   

Lu ta shaida, kuma ta yi farin cikin ganin ci gaban da asibitin ya samu cikin shekaru. A shekarar 1999, ta yi ritaya daga aiki. Ta kuma ki karbar damarmakin da aka ba ta dake da albashi mai yawa, daga manyan asibitoci a biranen Xi’an da Yulin. Zuwa Disamban 2018, Lu ta cika alkawarinta na taimakawa mazauna gundumar Jia inganta lafiyarsu cikin shekaru 50. Amma duk da haka ba ta huta ba, sai ma ci gaba da ta yi da aiki tukuru domin kula da lafiyar jama’a.

Cikin shekaru 20 da suka gabata, Lu ta samar da kulawar lafiya kyauta ga mazaunan da yawansu ya zarce 100,000.

Duk da shekaru sun ja, Lu na ci gaba da gudanar da aikinta a matsayin Likita. A shekarar 2019, ta amince da gayyatar da asibitin ya yi mata na duba marasa lafiya kyauta, sau daya a kowanne mako. “Ba zan iya tuna adadin marasa lafiya da na duba ba. Kamar jirgin leda, zan tashi zuwa ga marasa lafiya da zarar sun ja igiyar ledar,” cewar Lu.

A watan Mayun 2016, ta kafa wata kungiyar masu aikin sa kai da ya kunshi mutanen da suka manyanta, da zummar taimakawa mazauna yankin warware matsalolin rayuwa. Bisa kwarin gwiwar da suka samu daga Lu, mutane da dama sun shiga kungiyar.

Jim kadan bayan barkewar annobar COVID-19, a farkon 2020, Lu ta mika bukatar aiki a fagen daga. Ta rubuta a cikin bukatar cewa, “a duk inda ake bukata ta, zan hanzarta zuwa fagen daga ba tare da tsoro ba. Zan yi iyakar kokarina wajen sauke nauyin dake wuyana a matsayin Likita.” Domin taimakawa asibitin a aikin yaki da cutar, cikin kankanin lokaci Lu ta bayar da dala 1500 ga kungiyar JKS ta asibitin, a matsayin kudin mambar. Kuma ta ce, “ina fatan rayuwata za ta yi kyau kamar tarsatsin wuta, wadda ke fitar da karfi. Zan yi kokarin yayata ruhin Saniya, wajen hidimtawa jama’a da ingiza sabbin ci gaba da aiki ba tare da gajiyawa ba, yayin da nake bada gudunmuwata wajen inganta lafiyar mazauna.”

Bisa la’akari da nasarorin da ta samu, kungiyar mata ta kasar Sin ta karrama Lu da lambar yabo ta mace mafi fice a duk fadin kasar Sin, a shekarar 2021. Watanni 4 bayan nan kuma, kwamitin tsakiya na JKS, ya karrama ta a matsayin mambar jam’iyyar mafi fice. Duk da nasarorin da ta samu, Lu ba ta yi rayuwar almubazzaranci, kuma ta yi alkawarin ci gaba da kokarin taimakawa mazauna yankin inganta lafiyarsu.(Kande Gao)