logo

HAUSA

Rikicin Rasha da Ukraine ya fi shafar galibin kasashen Afirka da ke shigo da Alkama da mai

2022-04-18 15:56:57 CMG Hausa

Shugaban asusun Fairfax Africa, wani kamfanin zuba jari na kasa da kasa da ke Washington, Zemedeneh Negatu, ya bayyana yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya-bayan nan cewa, ana jin tasirin rikicin kasashen Rasha da Ukraine a duniya baki daya, amma tasirin yakin, ya fi shafar kasashen Afirka dake shigo da alkama da mai.

A cewar Negatu, takunkuman da Amurka da kawayenta suka kakabawa kasar Rasha, sun kara ta’azza hauhawar farashin kayayyaki a nahiyar Afirka, inda farashin man fetur da sauran kayayyakin masarufi ke tashi cikin sauri. (Ibrahim)