logo

HAUSA

Dakarun hadin gwiwa sun hallaka mayakan Boko Haram da na ISWAP sama da 100

2022-04-18 20:39:20 CMG Hausa

Rahotanni daga majiyoyin jami’an tsaro na cewa, dakarun hadin gwiwa na kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da Benin, sun kaddamar da hare hare kan maboyar ‘yan ta’addan Boko Haram da na ISWAP a yankin tafkin Chadi, lamarin da ya sabbaba mutuwar ‘yan ta’addan sama da 100.

Yayin farmaki kan mambobin kungiyoyin biyu, an hallaka a kalla manyan kusoshin su 10.  (Saminu)