logo

HAUSA

Najeriya da Nijar sun kai wa sansanin horaswar ISWAP hari ta sama

2022-04-17 16:05:36 CMG Hausa

Jaridar Daily Post ta tarayyar Najeriya ta wallafa wani rahoto dake cewa, a jiya Asabar 16 ga wata rundunar sojojin saman kasar ta bayyana cewa, kasashen Najeriya da Nijar sun dauki matakai na hadin gwiwa inda suka kai wa sansanin horaswar dakarun kungiyar ISWAP a yankin tafkin Chadi dake arewacin Najeriya hare-haren ta sama, tare da hallaka ‘yan ta’adda sama da goma, da kuma raunata wasu da dama. (Jamila)