logo

HAUSA

IOM: Mutum 6 sun mutu wasu 29 sun bace bayan nitsewar kwale-kwale a tekun Libya

2022-04-17 15:40:54 CMG Hausa

Hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa IOM, ta sanar a jiya Asabar cewa, an tsinci gawar mutane 6, sannan wasu mutanen 29 sun bace bayan da wani kwale-kwalen katako mai dauke da bakin haure 35 ya nitse a tekun yammacin Libya.

IOM tace, ana zaton bakin hauren da suka bace din sun riga sun mutu a hadarin kwale-kwalen da ya faru a ranar Asabar, a tekun birnin Sabratha na kasar Libya, sannan hukumar tace, jimillar mutane 53 ne aka bada rahoton mutuwarsu, ko kuma bacewarsu, a cikin makon da ya gabata.

IOM ta bayyana cewa, rayukan bil adama ba batu ne da za a yi sakaci dashi ba. Don haka hukumar tace akwai bukatar daukar karin matakai don bincikowa da kuma ceto rayukan, kana akwai bukatar daukar matakan gaggawa domin hana sake afkuwar mace-macen da ake samu da kuma wahalhalun da ake fuskanta.

Kasar Libya ta fada cikin yanayin tabarbarewar tsaro da tashe-tashen hankula, tun bayan mutuwar tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi, a shekarar 2011, inda kasar ta arewacin Afrika ta kasance a matsayin wata matattarar bakin haure dake tsallaka tekun Mediterranea zuwa kasashen Turai.

A cewar hukumar IOM, kawo yanzu, jimillar bakin haure 3,968 ne aka ceto kuma aka mayar dasu zuwa Libya a cikin wannan shekarar, wanda ya hada har da mata 375 da kananan yara 169.(Ahmad)