logo

HAUSA

Huawei Zai Taimakawa Kokarin Kenya Na Fadada Kayayyakin Sadarwar Intanet

2022-04-16 16:52:22 CMG Hausa

Katafaren kamfanin sadarwa na kasar Sin Huawei, zai hada hannu da gwamnatin kasar Kenya wajen bunkasa tsarin sadarwar ta hanyar fadada kayayyakin samar da su.

Kamfanin ya ce zai shimfida manyan wayoyin sadarwa na fiber cables masu tsawon kilomita 43,000 a fadin kasar domin bunkasa sadarwar intanet. .

Daraktan sashen harkokin kasuwanci na kamfanin Huawei a Kenya, Steve Kamuya, ya ce samar da hanyoyin sadarwar, zai fara ne da shimfida kilomita 25,000 na wayar fiber mai hade manyan yankunan da kanannan yankunan kasar ta hanyar hadin gwiwa da hukumar kula da fasahar sadarwa ta kasar.

Ya kara da cewa, daga baya kuma, za a shimfida karin wayar fiber mai tsayin kilomita 18,000 na karin ingancin sadarwar intanet, a wani kokari na cike gibin dake akwai a kasar.

Ita kuwa mataimakiyar daraktan sashen shirye-shirye na kamfanin Huawei a Kenya, Maureen Mwaniki cewa ta yi, zuba jari a kayayyaki masu amfani da inganta basira, shi ne jigon cike gibin dake akwai a kasar. Ta ce kamfanin Huawei ya gabatar da shirye-shirye a Kenya da nufin bunkasa ilimin fasahar zamani a tsakanin matasan kasar domin tabbatar da ana damawa da su wajen raya tattalin arziki dake mai da hankali kan ilimi. (Fa’iza Mustapha)