logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijer ya gana da ministan harkokin wajen kasar Nijer

2022-04-16 16:30:26 CMG Hausa

Jakadan Sin dake kasar Nijer, Jiang Feng ya gana da ministan harkokin waje da hadin gwiwa na kasar Nijer, Hassoumi Massaoudou, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashensu.

Jakada Jiang ya bayyana cewa, Sin da Nijer abokai ne da suka yi imani da juna, kuma kasashen biyu sun nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu, kana sun samu nasarori kan hadin gwiwarsu a dukkan fannoni. Ya ce, Minista Hassoumi Massaoudou ya yi shawarwari da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a kwanakin baya, inda suka tattauna kan sada zumunta da kara hadin gwiwarsu. Ya kara da cewa, Sin tana son hada hannu da kasar Nijer wajen zurfafa hadin gwiwarsu, da goyon bayan juna kan harkokin kasa da kasa don sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangare, minista Hassoumi Massaoudou ya yabawa danganatakar abota ta hadin gwiwa dake tsakanin Nijer da Sin, inda ya ce, kasar Sin muhimmiyar abokiya ce ga Nijer kan hadin gwiwa, wadda kuma ta samar da gudummawa sosai wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar. Ya ce yana farin ciki da musayar ra’ayoyi tsakaninsa da minista Wang Yi kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da batutuwan da suke mayar da hankali kansu, kana Nijer tana son kara imani da juna a tsakaninta da Sin a fannonin siyasa, da hadin gwiwa don raya dangantakar dake tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)