logo

HAUSA

An gano inda aka binne sarki Merenre

2022-04-15 01:04:34 CMG Hausa

A wurin binciken kayan tarihi na Saqqara dake kudancin birnin Alkahira na kasar Masar, masu binciken kayan tarihi na Masar sun gano inda aka binne sarki Merenre wanda ya mulki Masar a shekara ta 2270 kafin haihuwar Annabi Isa. Wajen binciken kayan tarihi na Saqqara wuri ne na Tarihin Duniya na UNESCO tare da dozin pyramids, binne dabbobi da tsoffin gidajen ibada na 'yan Koftik. (Bilkisu Xin)