logo

HAUSA

WHO: Har yanzu Afrika ba ta tsira daga barazanar COVID ba duk da raguwar yaduwar cutar

2022-04-15 13:51:26 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa, ya kamata kasashen Afrika su yi taka tsan-tsan, kuma su yi kyakkyawan nazari game da hadarin cutar gabanin sassauta matakan yaki da annobar COVID-19, duk da raguwar yaduwar cutar, WHO ta ce, nahiyar tana fuskantar barazanar yiwuwar sake barkewar sabon nau’in cutar.

Ofishin hukumar WHO na shiyyar Afrika ya bayyana cikin sanarwar cewa, hukumar ta bukaci kasashen Afrikan da su yi taka tsantsan, yayin da aka shafe tsawon lokaci ana samun raguwar yaduwar cutar mafi girma tun bayan barkewar annobar a nahiyar. Ta kara da cewa, a halin yanzu, adadin yaduwar cutar yana ci gaba da raguwa cikin makonni 16 da suka gabata, tun bayan da aka samu adadin mutane kusan 18,000 da suka kamu da kuma hasarar rayuka 239 a karshen mako na ranar 10 ga watan Afrilu, inda ake samun raguwar yaduwar cutar da kashi 29 da kuma kashi 37 bisa 100.

Matshidiso Moeti, daraktan WHO na shiyyar Afrika, ya bayyana fargaba na yiwuwar sake barkewar sabon nau’in cutar. (Ahmad)