logo

HAUSA

Ya Zuwa Yanzu Amurka Ta Kau Da Kai Daga Abin Bakin Ciki Da Ke Faruwa A Cikin Gidanta

2022-04-15 20:58:39 CMG Hausa

Kwanan baya, shehun malama a fannin ilmin doka Amy Wax daga jami’ar Pennsylvania ta kasar Amurka, ta soki Amurkawa ‘yan asalin Indiya a cikin wani shirin gidan telibijin na Fox News, inda ta ce, kasarsu ta kasance abin kunya. Kalamanta sun girgiza mutane sosai, kuma wani misali ne na yadda ake nuna bambanci ga Amurkawa ‘yan asalin kasashen Asiya a kasar Amurka.

Sin kullum Amurka ba ta kan yi shelar nuna daidaito a tsakanin kowa da kowa ba? Me ya sa Wax ta nuna wariyar launin fata a fili? Yau Jumma’a hukumar nazarin hakkin dan Adam ta kasar Sin ta kaddamar da rahoto mai taken “yadda ake nuna bambanci ga Amurkawa ‘yan asalin kasashen Asiya, ya nuna ainihin gaskiyar zaman al’ummar Amurka mai cike da wariyar launin fata”, wanda ya ba mu amsa.

Rahoton ya yi amfani da bayanai da misalai masu tarin yawa wajen bayyana cewa, kasar Amurka, wata kasa ce dake rinjayen fararen fata. Ana cin zalin Amurkawa ‘yan asalin kasashen Asiya da sauran ‘yan kananan kabilu a fannin hakkin dan Adam.

Cikin shekaru fiye da dari 2 da suka wuce, Amurka ta samu bunkasar tattalin arziki bisa kokarin da Amurkawa ‘yan kasashen waje. Amma gwamnatocin kasar ba su kula da su ba. ‘Yan siyasan kasar suna ikirarin kiyaye hakkin dan Adam da cimma mafarkin Amurka, ta hanyar cin zalin Amurkawa ‘yan kananan kabilu. (Tasallah Yuan)