logo

HAUSA

MDD tana maraba da sabuwar majalisar dokokin Somalia

2022-04-15 13:52:05 CMG Hausa

 

Jiya Alhamis MDD ta yi maraba da rantsar da sabbin mambobin majalisar wakilai da sanatoci da aka zaba a majalisun dokoki biyu na kasar Somalia.

Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya ce, bayan shafe sama da shekara guda da karewar wa’adin dukkan zababbun wakilai a kasar, a halin yanzu, ana farin cikin kafa sabuwar majalisar dokokin kasar.

Dujarric ya bayyana a taron ’yan jaridu cewa, MDD da abokan hulda, sun yi Allah wadai da harin ta’addanci, wanda kungiyar al-Shabaab ta dauki alhakin kaddamarwa, wanda ya faru a ranar Alhamis a kusa da wajen da aka yi bikin rantsuwar.

Ya ci gaba da cewa, MDD tana fatan za a gaggauta kammala raguwar shirye-shiryen zabukan kasar, musamman zaben shugabannin majalisun dokokin da na shugaban kasa. (Ahmad)