logo

HAUSA

Tsadar farashin kayayyaki ta tsananta a Ghana

2022-04-14 10:11:55 CMG Hausa

Hukumar kididdiga ta kasar Ghana, ta ce a watan Maris da ya shude, karuwar farashin kayayyaki a kasar ta ingiza hauhawar farashi, sama da wanda kasar ta taba samu cikin shekaru 12 da suka gabata.

Da yake tabbatar da hakan a jiya Laraba, babban jami’in kididdiga na kasar Samuel Kobina Annim, ya shaidawa manema labarai cewa, mizanin hauhawar farashin kayayyaki a watan Maris ya karu da kaso 3.7 cikin dari, inda ya kai maki 19.4 bisa dari, sama da maki 15.7 bisa dari da kasar ta samu a watan Fabarairu.

Hauhawar farashin kaya a watan Maris, wanda ya kai kaso 19.4 bisa dari, shi ne mafi yawa da kasar ta gani, tun bayan na watan Agustan shekarar 2009, lokacin da Ghana ta samu hauhawar kaso 19.7 bisa dari.

Mr. Annim ya alakanta karin da aka samu, da hauhawar farashin abinci da man fetur, wanda rikicin Rasha da Ukraine ya haifar.

Ya ce "Karuwar farashin abinci ya daga da kaso 22.4 bisa dari a shekara cikin watan Maris, daga kaso 17.4 bisa dari a watan Fabarairu. Kaza lika farashin kayayyakin da ba na abinci ba, shi ma ya karu da kaso 17 bisa dari a duk shekara a watan Maris, daga kaso 14.5 bisa dari a watan da ya gabaci hakan. Gudummawar farashin abinci da abubuwan sha da ba na barasa ba, sun daga farashin da kaso 2.0 bisa dari, daga kaso 49.4 bisa dari a watan Fabarairu, zuwa kaso 51.4 bisa dari a watan na Maris.  (Saminu)