logo

HAUSA

UNECA: Batun farfadowar Afirka daga COVID-19 zai ja hankali yayin taron tattaunawar ministoci dake tafe

2022-04-14 09:43:34 CMG Hausa

Hukumar raya tattalin arzikin nahiyar Afirka ta MDD UNECA, ta ce yayin taron karawa juna sani na ministocin kasashen Afirka dake tafe, za a maida hankali sosai ga batun farfadowar nahiyar daga tasirin annobar COVID-19.

Cikin wata sanarwa da UNECA ta fitar a jiya Laraba, ta ce taron ministocin ma’aikatun kudi, da tsare tsare, da bunkasa tattalin arziki na kasashen nahiyar, a bana zai gudana ne tsakanin ranekun 11 zuwa 17 ga watan Mayu dake tafe a birnin Dakar, fadar mulkin kasar Senegal.

Sanarwar ta kuma ce gibin kudaden samar da ci gaba ya fadada matuka, sakamakon barkewar annobar COVID-19, don haka ministocin da za su halarci taron, za su tattauna game da dabarun samar da kudaden farfadowar Afirka daga wannan mummunan yanayi.

Kaza lika UNECA, ta ce kudaden aiwatar da manufofin wanzar da ci gaban nahiyar Afirka a duk shekara, za su karu da kusan dala biliyan 154, sakamakon bullar COVID-19, da kuma karuwar kusan dala biliyan 285 cikin shekaru 5 masu zuwa, idan har ana fatan shawo kan kalubalen da annobar COVID-19 ta haifar. (Saminu)